Nigeria: Majalisa za ta binciki shugabanta Bukola Saraki

. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Majalisar dattawan Najeriya wadda Bukola Saraki ke jagoranta, tana takun-saka da shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali

Majalisar Dattawan Najeriya za ta binciki shugabanta Bukola Saraki kan shigo da wata motar da harsashi ba ya ratsa ta ta miliyoyin kudi, ba bisa ka'ida ba.

Matakin yin binciken ya zo ne bayan tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Ali Ndume, ya nemi a yi bincike kan zargin da ake yi cewar Bukola Saraki ya shigo da motar kasar ba bisa ka'ida ba, abin da ya sa hukumar hana fasa-kauri ta kasar, wato Kwastam ta kwace motar.

Zaman majalisar wanda mataimakin shugabanta Ike Ekweremadu ya jagoranta, ya nemi kwamitin da'a na majalisar ya yi bincike kan zargin ya kuma bayar da cikakken rahoto.

Amma shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki, ya musanta zargin.

Mai magana da yawun Saraki, Yusuph Olaniyonu, ya ce, an sayi motar ne don amfanin majalisa.

Ya kuma ce, "Majalisar ta bayar da kwangilar sayo motar ne ta hannun wani dan kwangila, sai hukumar Kwastam ta kwace motar a lokacin da yake neman kai ta Abuja daga birnin Legas."

"Mun yi imanin cewar lamari ne tsakanin dan kwangilar da kuma hukumar Kwstam, saboda majalisar ba ta karbi motar ba har yanzu. Me ya sa wani yake neman saka sunan Saraki cikin batun?" In ji Mista Olaniyonu.

A wata sanarwar da ya aika wa BBC, Yusuph ya kara da cewa: "Takardun motar na nan domin mutane su gani su yanke hukunci da kansu. A yanzu da aka riga aka kai batun gaban kwamitin da'a, gaskiya za ta bayyana."

Har wa yau majalisar ta umurci kwamitin da'arta da ya binciki zargin da ake yi wa Sanata Dino Melaye na amfani da takardar shaidar kammala digiri ta bogi da ake zargin yana amfani da ita.

Dama dai a baya-bayan nan Majalisar dattawan tana takun-saka da shugaban hukumar Kwastam, Hameed Ali, wanda take son ya bayyana a gabanta cikin kayan sarki domin yin wasu bayanai game da manufofin hukumar.

Sai dai Kanal Ali mai ritaya ya da farko ya ce yana da uzuri ba zai samu zuwa ba, amma daga baya ya je. Sai dai 'yan majalisar ba su saurare shi ba sun tsaya kai da fata cewa sai ya sa kakin hukumar Kwastam din.

Ana sa ran dai zai sake bayyana a gaban majalisar a ranar Laraba.

Labarai masu alaka