Trump zai budewa 'yarsa ofis a fadar White House

Ivanka da maigidanta Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ivanka za ta yi aiki ne a matsayin idanu da kunuwan Donald Trump yayinda za ta rika shawarwar

Shugaba Donald Trump zai budewa 'yarsa, Ivanka ofishi a fadar White house a cewar wani jami'in fadar. Sai dai ba za a bata wani matsayi ko albashi ba a hukumance idan ta fara aiki a bangaren yammacin fadar.

Jami'in ya tabbatar da wasu rahotonnin kafafen watsa labarai da ke cewa za a bai wa Ivanka 'yar shekara 35 din damar samun bayanan fadar da ba kowa ne zai iya samu ba.

An ambato Atoni janar dinta na cewa, "za ta yi aiki ne a matsayin idanu da kunnuwan Donald Trump yayin da za ta rika bayar da shawarwari."

Ivanka, wacce ke da kamfanin sayar da kayan kawa, za ta yi aiki tare da mijinta wanda yake a matsayin babban mai bai wa shugaban kasar shawara.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A makon da ya gabata ne dai Ivanka ta zauna kusa da shugabara gwamnatin Jamus, Angela Merkel, a lokacin da ta kai wata ziyara Amurka

Ma'auratan biyu na yin tasiri a kan al'amuran shugaban Amurkar, kuma hakan yasa mutane ke ganin kamar zai jawo hamayyya tsakanin manufofin gwamnati da nasu bangaren.

Lamarin ya kuma jawo muhawara kan ko akwai wani takunkumi tsakanin siyasar iyalin Mista Trump da ayyukan kasuwancinsu.

Ivanka dai na halartar ganawa da shugabanin duniya, wadanda suka hada da Firai ministan Canada Justin Trudeau, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, tun bayan da Mista Trump ya karbi ragamar mulkin.

Labarai masu alaka