Nigeria: An kashe akalla mutum 32 a Zaki Biam ta Benue

Kasuwa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kama mutum uku wadanda ake zargi suna da hannu a harin da aka kai

A kalla mutum 32 ne suka mutu a garin Zaki Biam da ke karamar hukumar Ukum na jihar Benue, da ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriya.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari wata kasuwar doya a garin Zaki Biam da ke jihar.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Moses Yamu ya ce mutum 17 ne suka mutu yayinda wasu 11 suka jikkata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin, ya kuma mika sakon ta'aziyyarsa ga 'yan uwan wadanda harin ya shafa.

Mai magana da yawun shugaban Femi Adesina, ya ce, "Shugaba Buhari ya umarci jami'an tsaro su fara binciken gaggawa da nufin hukunta wadanda suka aikata laifin".

Moses Yamu ya shaida wa BBC cewa, "Da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Litinin ne wasu mutane a cikin mota da kuma wasu a kan babura suka shiga garin kuma suka bude wa wasu 'yan kasuwa wuta".

Ya kara da cewa tuni an kara tsaurara matakan tsaro a yankin kuma tuni aka kama mutum uku wadanda ake zargin suna da hannu a harin.

Lamarin dai na zuwa ne mako guda bayan wasu wadanda ake zargin Fulani makiyaya ne sun kashe sama da mutum 10 a yankin Buruku da ke Jihar, wanda hakan yasa gwamnan jihar, Samuel Ortom ya basu umarnin su bar yankin a cikin kwana uku.

Ana yawan samun rikicin manoma da makiyaya a wasu jihohin kasar da suka hada da Benue.

Labarai masu alaka