Gyara-kayanka El-Rufa'i ya yi wa Buhari — Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Hakkin mallakar hoto facebook
Image caption Attahiru Dalhatu Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto a Najeriya, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ce shi bai ga laifin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi ba saboda ya rubuta wa shugaba Buhari wasikar gyara kayanka.

A baya-bayan nan ne dai wata wasikar da Nasir El-Rufa'i ya rubuta wa shugaban Muhammadu Buhari, a watan Satumbar 2016, ta bayyana.

A cikin wasikar, El-Rufa'i ya nemi shugaba Buhari da ya yi karatun ta-nutsu wajen aiwatar da ayyukan alherin da jam'iyyar APC ta alkawarta wa al'ummar Najeriya.

Duk da wannan wasikar ta haifar da kace-nace a kasar, a inda wasu ma ke ganin beken El-Rufa'i, shi kuwa Alhaji Bafarawa ya ce sam gwamnan na Kaduna ba shi da laifi.

Attahiru Bafarawa ya kuma kara da cewa tun da jam'iyyar PDP ta gaza, ya kamata a ce APC mai mulki ta fitar da 'yan Najeriya daga halin da suke ciki.

Ga dai yadda hirar Attahiru Bafarawan ta kasance da Yusuf Tijjani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Attahiru Dalhatu Bafarwa