Gyara kayanka Elrufa'i ya yi wa Buhari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Alhaji Bafarwa ya ce sam gwamnan na Kaduna ba shi da laifi.

Tsohon gwamnan jihar Sokoto a Najeriya, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ce shi bai ga laifin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir Elrufa'i ya yi ba saboda ya rubuta wa shugaba Buhari wasikar gyara kayanka.