Kun san 'ya'yan shugabannin da ke da karfin fada a ji a duniya?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ivanka Trump dama can shahararriyar 'yar kasuwa ce

A yayin da aka budewa Ivanka Trump ofishinta na kashin kanta a fadar White House, ta kuma zamo 'yar shugaban kasa ta baya-bayan nan da za ta dinga bai wa mahaifinta shawara a harkar mulki, BBC ta yi duba kan 'yan'yan shugabannin kasashen duniya da suka yi fice kuma masu karfin fada a ji a duniya.

Samun ofis da Ivanka Trump ta yi a fadar gwamnatin Amurka, ya sake daga darajarta, ya kuma nuna cewa tana daga cikin matan da ke da karfin fada-a-ji a gwamnatin Donald Trump.

Matashiyar 'yar shekara 35 za ta yi aiki ne a matsayin 'kunnuwa da idanun mahaifinta,' amma ba za a biya ta albashi ba, a sabon aikin nata.

Ivanka, wadda 'yar kasuwa ce kuma shahararriya sosai, ita ce ta baya-bayan nan a jerin sunayen 'ya'yan shugabannin kasashe masu karfin fada a ji a duniya.

Wakiliyar BBC Valeria Perasso, ta yi duba kan irin rawar da wadannan 'ya'ya suke takawa a harkar mulkin iyayensu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Maryam Nawaz Sharif pta taka rawa a yakin neman zaben Babanta

Iyali cikin al'amuran siyasa

Maryam Nawaz Sharif, mai shekara 43 'ya ce ga Firai ministan pakistan Nawaz Sharif.

A yanzu haka kuma tana yi wa jam'iyyarsa ta 'Right-wing Pakistan Muslim League aiki.

Wakilin BBC Asif Farooqi, wanda ya yi hira da ita a lokuta da dama ya ce, "Ko da yaushe tana mayar da hankali a kan abin da take yi." Ya kara da cewa, "Ta zama wata mai karfin fada a ji, ko kuma a iya kiranta da kunnuwan mahifinta.

A shekarar da ta gabata ne aka ayyana sunanta a wasu takardun da aka fallasa na jerin sunayen masu boye dukiya a tsibirin Panama, inda aka zarge ta tare da 'yan uwanta biyu da alaka da wadansu kamfanoni

Mahaifinta ya karyata zargin, inda ya ce, "Kawai aikin 'yan adawa ne masu son bata min suna tare da iyalaina a harkokin siyasa."

Babbar kotun Kasar Pakistan dai ta saurari kararrakin da suka danganci wadannan zarge-zarge, kuma ana tsammanin za ta yanke hukunci a makonnni masu zuwa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yekaterina tana son harkar rawa

Fitacciyar 'yar rawa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin sananne ne wajen kare rayuwar iyalansa, sai a baya-bayan nan ne ma aka fara sanin wani abu da ya danganci 'ya'yansa mata biyu.

Wakilin BBC a Rasha Famil Ismailov ya ce, "Jami'an kasar suna matukar sanya alamar tambaya da zargi kan duk kafar yada labaran da ta nuna sha'awar yin wani labari da ya shafi 'yan matan."

Ya kara da cewa, "Ya rage wa 'yan jaridar su lalubo hanyar da za su samu bayanai sosai a kan 'ya'yan shugaban, kuma mafi yawan bayanan da ake samu a kansu, ba daga bakin iyali suke fitowa ba.

A shekarar 2015 ne aka sake sanin wata karamar 'yarsa Yekateria, bayan da ya bayyana cewa tana zaune a birnin Moscow tana amfani da sunan Katerina Tikhonova.

Daga wannan lokacin ne kuma 'yan kasar suka gane cewa tana auren wani hamshakin dan kasuwa ne mai suna Kirill Shammalov, wanda kuma da ne ga daya daga cikin tsofaffin abokan mahaifin nata. kuma ma'auratan na samun a kalla dala biliyan biyu ta hanyar zuba jari a kamfanonin Gas da na danyen man fetur.

Matashiyar tana 'yar shekara 30, tana tafiyar da wani asusun gwamnati wanda zai gudanar da ayyukan ci gaba a Jami'ar Moscow.

An dai bayar da rahotonnin cewa tana lura da kwangilolin miliyoyin daloli a kasashen waje, kuma tana daga cikin masu bai wa shugaba Putin shawara.

TIkhonova kuma wata 'yar gasar rawa ce, wacce ta zo ta biyar a gasar rawa ta duniya da aka gabatar a shekarar 2013 a kasar Switzerland.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ms Dos Santos

Ta gaban goshin shugaban Angola

Isabel dos Santos mai shekara 43 ita ce babbar 'yar shugaban kasar Angola Jose dos Santos, wanda yake mulkin kasar tun shekarar 1979.

Ita ce shugabar kamfanin man kasar wato Sonangol kuma a shekarar 2013 ne wata mujalla mai suna "Forbes" ta ayyana ta a matsayin matar da ta fi ko wacce mace arziki a Afirka, inda ta mallaki dala biliyan 3.2.

Miss Dos Santos wacce ta yi karatu a Birtaniya, tana da hannun jari a bankunan kasar da kamfanonin sadarwa da kuma kamfanin kera daiman, wanda hakan ya sa ta zama daya daga cikin shahararrun 'yan kasuwar Angola.

Kuma tana hannayen jari a bangaren wutar lantarki, da bangaren man fetur da iskar gas, a kasar Portugal, wacce ita ce kasar da ta yi wa Angola mulkin mallaka.

A kasar da kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta bayyana a matsayin ta gaba-gaba a cin hanci da karbar rashawa, Miss Dos Santos na fuskantar zargin cewa ta samu dukiyarta ne da matsayin mahaifinta. Zargi ne kuma da ita da masu ba ta shawara suka sha musantawa.

Ta bayyanawa BBC a shekara 2015 cewa, "Nasarar da na samu a yau, ba abu ba ne da yazo min dare daya, wani abu ne da na dauki shekaru ina tanadinsa"

Hakkin mallakar hoto Turkish Presidency/Y. Bulbul/Anadolu Agency/Getty
Image caption Sumeyye Erdogan ta auri Selcuk Bayraktar wani fitaccen dan kasuwa

Shalelen Babanta

Sumeyya Erdogan, mai shekara 31, ita ce karamar 'yar shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, kuma da yawa ana yi mata kallon wacce ya fi so.

Wakilin BBC a Turkiyya Irem Koker ya ce, "Mahaifinta na kiranta da Barewata". A Turkiyya wannan kalmar na nufin, 'kyakkyawan abu da ake matukar so.''

Yarinyar, wadda ta karanta kimiyyar siyasa a Amurka da Birtaniya, ta zama mai bayar da shawara ga mahaifinta lokacin da ya shugabanci Jam'iyyar AKP, kuma ta sha yi masa rakiya a tafiye-tafiyen diflomasiyya da yake yi.

A shekarar 2015 an yi ta yada jita-jitar cewa za ta tsaya takara a majalisar kasar, sai dai kuma ba ta yi hakan ba.

A yanzu haka dai tana taka rawa a wata kungiyar rajin kare hakkin mata ta kasar .

Baya ga aikin yakin neman zabe, Sumeyye ta ci gaba da zama sojar baka ga mahaifinta da kuma gwamnatinsa

Hakkin mallakar hoto PRESIDENCY OF THE REPUBLIC OF TAJIKISTAN
Image caption Ozoda Rahmon

'Yar shugaban kasar Tajikistan

Ozoda Rahmon, mai shekara 39 'ya ce ga dadadden shugaban Tajikistan Emomali Rahmon.

Tana da Digiri a fannin shari'a, ta kuma fara aiki a bangaren diflomasiyya, kafin daga bisani ta zama mataimakiyar ministan kasashen wajen kasar, a shekarar 2009.

A shekarar 2016 mahaifin nata ya nada ta shugabar ma'aikatan fadar gwamnatinsa kuma an zabe ta a majalisar dattawan kasar.

Ozoda na auren Jamoliddin Nuraliyev, mataimakin shugaban babban bankin Tajikistan, kuma suna da y'a'ya biyar.

Ba ita kadai ce ke rike da mukamin gwamnati ba a cikin zuri'ar. Babban wanta Rustam shi ne magajin garin babban birnin kasar Dushanbe, kuma kanwarta Rukhshona na aiki da ma'aikatar harkokin kasashen waje.

Rahotanni sun ce sauran 'yan uwanta ma na rike da manyan mukaman gwamnati da harkokin kasuwanci, al'amarin da ya sa zuri'ar Rahmon suka zamo cikin manyan masu arzikin kasar a Tajikistan.

Hakkin mallakar hoto Johnny Nunez/ WireImage/ Getty Images
Image caption Mariela diyar Raul Castro mai fafutukar kare masu luwadi da madigo ce

'Yar shugaban Cuba

A matsayinta na diyar shugaban kasar Cuba Raul Castro, Mariela Castro 'yar wan tsohon jagoran juyin juya hali ne Fidel.

Wakilin BBC ya ce, "Ana ganin mahaifiyarta Vilma Espin a matsayin wata mai fafutukar kare hakkin mata, kuma a yanzu ana ganin kamar ta biyo sawun mahaifiyar tata ne.

An haifeta a shekarar 1962, Ms Castro 'yar majalisar dokoki ce da ba ta shayin fadar abin da ke ranta, kuma tana fafutukar kare hakkin tsirarun mutane marasa galihu.

An san ta sosai kan fafutukar neman 'yancin masu luwadi da madigo a kasar.

Labarai masu alaka