Nigeria: Bam ya hallaka mutane a sansanin 'yan gudun hijira

Bomb
Image caption Hare-hare na karuwa a Maiduguri a baya-bayan nan

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya na cewa, a kalla mutum hudu ne suka mutu, yayin da wasu 18 kuma suka jikkata, sakamakon tashin bam a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Damian Chukwu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce bama-bamai biyu ne suka tashi a sansanin.

Ya ce al'amarin ya faru ne da misalin karfe 4.30 na asubahin ranar Laraba.

Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa sun ji karar fashewar bam sau uku, biyu a sansanin 'yan gudun hijira, dayan kuma a wata unguwa kusa da sansanin, duk a kusa da tashar Muna.

Wadannan hare-hare dai su ne na baya-bayan nan da aka kai a birnin.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne wani bidiyo ya fara yawo a shafukan sada zumunta inda wani da ya yi ikirarin shi shugaban kungiyar Boko Haram ne yake cewa su suke kai hare-hare a Maiduguri, da kuma wani hari da aka kai wani gari kusa da birnin a makon da ya gabata.

An kuma sake kai wani harin ranar Lahadi da ya yi sanadin mutuwar mutum hudu.

Yawan kai hare-hare ya karu a Maiduguri tun a karshen shkerar 2016, duk kuwa da ikirarin da sojojin Najeriya ke yi cewa suna samun galaba a yakin da suke da kungiyar Boko Haram.

Jihar Borno dai za a iya cewa nan ce hare-haren kungiyar Boko Haram ya fi yi wa illa, kuma kiyasi ya nuna cewa kusan mutum 15,000 ne suka mutu sakamakon rikicin kungiyar, yayin da fiye da mutum miliyan biyu kuma aka tilasta su barin muhallansu.

Labarai masu alaka