Yadda BBC ta yi tasiri a rayuwar Inyamurai
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda BBC ta yi tasiri a rayuwar kabilar Ibo

Albarkacin bikin cikar BBC Hausa shekara 60 da kafawa, mun leka yankin kudu maso gabashin Najeriya inda ko a sashen Hausa na BBCn yake da dumbin masu sauraro, ba wai 'yan arewacin kasar mazauna yankin kadai ba, har ma da 'yan kabilar Ibo, wato 'yan asalin yankin, wadanda su ma suka rungumi al'adar sauraren rediyo.

Wakilinmu a Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya duba yadda sauraren sashen Hausa na BBC ya yi tasiri ga rayuwarsu, ga kuma rahotonsa.