China: Yara sun mutu a kokawar shiga bandakin makaranta

A map showing Puyang, Henan province, China

Kafar yada labari ta kasar China ta bayyana cewa, an samu mutuwar yara biyu da jikkatar yara 20 sakamakon turmutsutsun da ya faru a wata makarantar firamare da ke yankin tsakiyar kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ce, daliban sun cika ne makil a bandaki lokacin da suka fito tara a garin Puyang, sai aka fara turereniya don samun hanyar fita.

A wani rahoton da wata jaridar kasar China ta fitar, ta yi da'awar cewa katangar bandakin ce ta rushe sakamakon turereniyar da aka yi.

An garzaya da wadanda suka jikkata asibiti, kuma rahotanni sun ce da yawa daga cikinsu, suna cikin matsanancin hali.

Gwamnatin gundumar Puyang ta shaida wa kamfanin dillancin labari na AP cewa, ana bincike a kan faruwar lamarin, amma ba su bayar da cikakken bayani ba.

Al'amarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba a Makarantar Firamare ta "Experimental" a garin Puyang, da ke lardin Henan.

An sha samun faruwar irin haka a baya.

A shekarar 2014 ma an samu mutuwar yara shida, wasu 25 din kuma sun jikkata a wata makaranta yayin da ake turereniya a matattakalar bene, a Kudu-maso Yammacin China..

Labarai masu alaka

Karin bayani