'An kama 'yan Boko Haram a Ekiti'

Sojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojin Najeriya sun sha alwashin murkushe Boko Haram

Hukumomin tsaro a Najeriya sun ce sun kama wani dan kungiyar Boko Haram a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin kasar.

A wata sanarwa da babban jami'in hukumar tsaron farin kaya, DSS, Tony Opuiyo ya fitar, ya ce dakarunsu sun gudanar da farmaki a sassa daban-daban na kasar inda suka kama 'yan ta'adda da masu son tayar da zaune tsaye da dama.

Ya kara da cewa a ranar Litinin ne hadin gwiwar rundujar soji da ta DSS ta kama mutumin da ake zargi dan Boko Haram ne mai suna Adenoyi Abdulsalam a birnin Ado Ekiti.

A cewarsa, kafin a kama Abdulsalam, "an kai farmaki kan mayakan Boko Haram da dama a arewacin kasar da suka hada da Bauchi, Yobe, Gombe, Nasarawa, Kaduna da Kogi".

Mista Opuiyo ya kara da cewa cikin wadanda aka kama har da wani dan Boko Haram Usman Ladan Rawa, wanda ake yi lakabi Mr X a Lafia, jihar Nasarawa.

Kazalika, an kama wani dan Boko Haram din mai suna Nasiru Sani, wanda ake yi wa lakabi Osama a Bauchi yayin da aka kama wani dan Boko Haram din Adamu Jibrin.

Sanarwar ta kuma ce Abdulazeez Umaru da Nuhu Usman, wasu 'yan Boko Haram din a jihohin Yobe da Kogi.

Sauran 'yan Boko Haram da DSS ta ce ta kama sun hada da: Suleiman Yahaya, wanda ke cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo a jihar Yobe da Mohammed Isyaka, wanda aka kama a Kano da Uwais Abubakar, Abdullahi Umaru da kuma Mukhtar Suleman, wadanda aka kama a Kogi.

Haka kuma an kama Ali Bukar da Mustapha Umar su ma a jihar Kano, yayin da aka cafke Abdullahi Isah a birnin Lafia na jihar Nasarawa saboda kitsa hare-hare.

Hukumar DSS ta ce ta kuma kama wani kwamandan Boko Haram Ibrahim Fulata da abokan aikinsa - Shamsudeen Aliyu, Zaharadeen Ibrahim da kuma Suleiman Abubakar a Bauchi.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da alakar mutanen da kungiyar ta Boko Haram.

Baya ga 'yan Boko Haram, DSS ta ce ta kamata masu tayar da zaune tsaye da dama a wasu jihohin.

Boko Haram ta kashe dubban mutane a Najeriya da kuma raba miliyoyi da gidajensu.

Labarai masu alaka