An ga miciji a cikin jirgin sama a Alaska

Wata ma'aikaciyar cikin jirgin sama da macijin da ka gano Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Macijin na bacci a lokacin da aka gano shi a cikin jirgin saman

An gano wani maciji da wani mutum ya manta shi a wurin ajiyar kaya a cikin jirgin sama, wanda mutumin ya ce ya shaƙu da shi sosai.

Matukin jirgin ya sanarwa da fasinjojin cewa: "Akwai miciji a cikin jirgin nan sai dai bamu san inda yake ba".

Wani yaro ne da ya tashi ya tsaya kan kujerarsa a cikin jirigin saman ya gano macijin mai launin ruwan dorawa, amma kuma mara guba ne.

A lokacin da ya ganshi, macijin na bacci kuma wata jaka da ke bayan jirgin ta dan rufe shi.

A cewar mahaifiyar yaron, Anna McConnaughy, mutanen da ke cikin jirgin ba su daga hankali ba sosai.

Ta kara da cewa wani matukin jirgin yazo ya tattauna da mutanen dake cikin jirgin saman kan yadda za a kamo macijin.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Da farko dai a karshin wata jaka aka gano macijin

Sai wani ma'aikacin jirgin ya kamo cikin macijin ya saka shi a cikin wata ledar shara.

A cikin wani kwadon shara aka saka micijin bayan an daure shi a leda sai aka dora shi sama kusa da inda ake ajiyan kaya.

Tun da fari aka sanar da ma'aikatan cikin jirgin cewa akwai maciji a cikin bayan da wani ya sanar cewa macijinsa ya bata bayan da ya sauka daga cikin wani jirgin sama da zai je Aniak da ke Alaska.

Mai macijin ya kara da cewa akwai yiwuwar yana cikin jirgin da zai koma birnin Anchorage da ke garin Alaska.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ba a tabbatar da kowane irin maciji bane

Mai magana da yawun kamfanin jirgin sama na Ravn Alaska, William Walsh ya ce sun ji dadi da aka ankarar da su amma ya kuma kara da cewa mai macijin ya saba doka, da bai sanar cewa zai hau jirgin da maciji ba.

Bai tabbatar da kowane irin maciji bane ko an ci tarar shi wasu kudade.

Labarai masu alaka