Cambodia: Mata na sayar da ruwan mama don neman kudi

Wani kamfanin sayar da ruwana mama a Cambodia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana sayar da kowane fatiki na ruwan maman kan dala 20

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta yi Allah wadai da sayar da ruwan Mama da mata a Cambodia ke yi saboda su samu kudi.

A farkon makon nan ne hukumomin kasar suka dakatar da fitar da ruwan maman da ake yi zuwa kamfanin Ambrosia da ke Amurka.

Kamfanin dai ya yi ikrarin cewa shi ne kamfani farko da ya fara fitar da ruwan mama daga wata kasar zuwa Amurka.

Hukumar ta shaida wa BBC cewa, ruwan mama tamkar jinin da ke jikin dan Adam ne, kuma bai kamata a goyi bayan sayar da shi ba.

UNICEF din ta ce tamowa na ci gaba da barazana ga lafiyar yara a Cambodia, kuma hukumar ta ce ruwan mama na da matukar amfani ga lafiyar yara.

An yi amannar kamfanin Ambrosia na biyan matan Cambodia sama da dala shida a ko wacce rana domin tatsar ruwan mama.

Ana saka ruwan maman a firiji ya yi kankara, sannan sai a kai Amurka a sayar da ko wane fakiti daya wanda za a iya shayar da jariri sau biyu kan dala 20.