PDP ta dinke baraka don kwace mulki daga APC

Sanata Ali Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Bangarorin biyu sun dade suna rikici kan shugabancin jam'iyyar

Bangarorin da ke rikici da juna a babbar jam'iyyar adawa ta PDP, sun ce za su rungumi turbar sulhu da zaman lafiya domin kwace mulki daga jam'iyyar APC ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Bangaren Sanata Ali Modu Sheriff da Ahmed Makarfi sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar da za ta kai ga sasanta rikicin shugabancin da suka dade suna yi.

Sanarwar da bangarorin suka fitar, ta umarci dukkan masu ruwa a rikicin da su daina yin maganganun da za su rura wutar rikicin, sannan kuma su goyi bayan shirin sulhu da Gwanman Bayelsa, Seriake Dickson ke jagoranta.

Sai dai sanarwar ba ta yi bayani kan shari'ar da ke gaban kotun kolin kasar ba, inda Sanata Makarfi ke kalubalantar hukuncin da ya bai wa Sanata Sheriff nasara.

A cewar sanarwar: "Bai kamata jam'iyyar ta rinka bata lokacinta wurin fadan cikin gida ba, maimakon hada kan 'ya'yanta da kuma samar da adawa mai karfi wadda za ta kai ga kwace mulki daga gwamnatin APC da ta gaza".

Bernard Mikko da Ahmed Gulak daga bangaren Sheriff da kuma Dayo Adeyeye da Dave Iorhemba daga bangaren Makarfi su ne suka sanya hannu a kan jarjejeniyar.

A baya dai an yi irin wannan yunkuri ba tare da samun nasara ba.

Tun bayan da ta sha kaye a zaben 2015, jam'iyyar PDP wacce ta shafe shekara 16 tana mulkin Najeriya, ta fada cikin rikicin shugabanci.

Lamarin da ya haifar da shari'a a matakai daban-daban, sannan ya raba kawuna 'ya'yan jam'iyyar, wacce a baya ake wa kallon gagara-badau.

Wannan kuma ya sa 'ya'yan jam'iyyar da dama sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Lamarin ya kuma sa an rasa wata cikakkiyar jam'iyyar adawa da za ta sa ido kan ayyukan jam'iyya mai mulki.

Masu sharhi na ganin muddum ba su hade wuri guda ba, to ba za su iya yin wani tasiri kan jam'iyyar APC ba.

Labarai masu alaka