Allah Ya yi wa Ahmed Kathrada na Afirka ta Kudu rasuwa

Ahmed Kathrada. Photo: December 2013 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ahmed Kathrada ya shafe shekara 26 a gidan yari

Allah Ya yi wa fitaccen dan siyasar Afirka ta Kudun nan Ahmed Kathrada, rasuwa yana da shekara 87.

Cibiyar Mista Kathrada, wacce ke kula da al'amuransa, ta ce ya mutu ne a asibitin Donald Gordon a birnin Johannesburg bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Shi dai makusanci ne ga marigayi tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela, kuma tare suka yi zaman sarka a tsibirin Robben bayan yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai a 1964.

An same su ne da laifin yunkurin kifar da gwamnatin farar fata mai mulkin nuna wariya.

Mista Kathrada ya shafe shekara 26 a gidan yari, 18 daga ciki a mummunan gidan yarin nan na Tsibirin Robben.

An sallame shi a 1989, kuma daga nan ne Shugaba Mandela ya nemi shi da ya zo su yi aiki tare a gwamnati.

Ahmed Kathrada ya bar majalisa a 1999, sai dai ya ci gaba da taka rawa a fagen siyasa.

Ya kuma soki yadda ake gudanar da al'amura a jam'iyyar ANC sannan ya nemi Shugaba Jacob Zuma ya yi murabus.

Marigayin, wanda Musulmi ne, ya yi fice wurin goyon bayan fafutikar kafa kasar Palasdinu.

Labarai masu alaka

Labaran BBC