Masu zanga-zanga sun bai wa Amnesty kwana uku ta bar Nigeria

. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar Amnesty Internatiional daya ce daga cikin kugiyoyin kare hakkin bil adama na duniya.

Wasu masu zang-zanga a Abuja, babban birnin Najeriya sun nemi kungiyar Amnesty International da ke fafatukar kare hakkin bil adama ta bar kasar cikin sa'o'i 72.

'Yan kungiyar Global Peace and Life Rescue Initiatives , wadda ta shafe kwana uku tana zanga-zangar kin kungiyar Amnesty International, ta ce ta yi hakan ne domin kare martabar jami'an tsaron Najeriyar.

A gangamin da 'yan kungiyar suka yi ranar Laraba sun fita da akwatin gawa wanda aka rubuta wa 'Allah jikan Amnesty International' inda suka yi ta wakokin kin kungiyar.

Shugaban masu zanga-zangar, Melvin Ejeh, ya ce kungiyar Amnesty International na sukar jami'an tsaron Najeriya a rahotanninta kuma ba ta kula da aika-aikar da masu tayar da kayar baya ke yi.

Ya kara da cewar dole kungiyar ta daina abin da ya kira aikin rashin mutunci kan 'yan kasar, yana mai karawa da cewar kungiyarsa za ta bi duk hanyar da doka ta yarda da ita wajen korar Amnesty International din.

Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin kungiyar da ke fafatukar kare hakkin bil adaman, sai jami'in hulda da jama'a na Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce kungiyar ba za ta mayar da martani ga masu zanga-zangar ba domin ba a san da zamansu ba.

Amma wani tsohon mai fafatukar kare hakkin bil adama, Sanata Shehu Sani, ya ce bai dace a nemi korar kungiyar Amnesty International daga Najeriyar ba domin kungiya ce da ake mutuntawa a fagen kare hakkin jama'a a kasashen duniya.

Ya kara da cewar babu son kai a rahotannin da kungiyar ke fitarwa domin suna bayyana abubuwan da jami'an tsaro ke yi da kuma abubuwan da masu tayar da kayar baya ke yi.

Labarai masu alaka