'Mun san wanda ya kai harin ta'addanci a London'

Image caption 'Yan sanda na kai-komo a ginin majalisar Westminster

'Yan sandan birnin London sun ce suna da bayanai kan mutumin da ya kai harin a majalisar dokokin Burtaniya da ke birnin Landan, ranar Laraba abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu da jikkata da dama.

Mutumin dai ya kutsa cikin mutane da mota a kan gadar masu tafiya a kasa ta Westminster, kafin daga bisani ya gangaro zuwa ginin majalisar dokokin kasar.

Sai dai kuma 'yan sandan ba su bayar da karin bayani ba kan maharin duk da sun ce suna da bayanai a kansa.

Kawo yanzu dai jami'an tsaron sun ce harin ya yi kama da na masu kaifin kishin Islama.

Tsohon ministan kasashen wajen Poland, Radoslov Shikoski, ya ce ga yadda al'amarin ya faru, a lokacin yana cikin Taxi.

"Na ji wani abu da na tsammaci kawai karon motoci ne amma bayan da na kallaci abun ta gilashin taxin da nake ciki, sai kawai na ga wani mutum a kasa tare da alamar damuwa."

"Daga nan kuma na kara ganin mutum na biyu sai na fara daukar hoto sai kuma na ga mutane uku a kasan gada suna zubar da jini babu kakkautawa, a takaice dai abun da na gani hatsari ne da ya rutsa da mutane biyar da suka samu munanan raunuka."

Tuni dai aka fara nuna alhinin rashin mutanen.

Image caption An fara sanya furanni a wurin da aka kai harin na Landan

Shugabannin kasashen duniya sun fara aike wa da sakon alhini ga firai ministar Burtaniya, Theresa May.

Shugaban kasar Faransa, Francoise Hollande da firai ministan Spaniya, Mariano Rajoy da na Australia Malcolm Turnbull da kuma shugaban Amurka, Donald Trump sun yi alkawarin taya Burtaniya yaki da ta'addanci.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani mutumin da ake zargi da kai harin ya samu kulawa

An bude zauren Majalisar Burtaniya bayan harin ta'addancin da aka kai majalisar da ke birnin Landan ranar Laraba.

'Yan Majalisun da ke cikin majalisa a lokacin da aka kai harin sun wallafa sakonni a shafukansu na Twitter na cewar sun samu fita inda suka jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su.

Magajin garin Landan, Sadiq Khan, ya ce Landan ba za ta razana da aikin ta'addanci ba.

Ya ce za a tura karin jami'an tsaro a titunan birnin Landan cikin daren Laraba.

Hasarar Rayuka

Rundunar 'yansandan Burtaniya ta ce mutum hudu ne suka mutu, cikinsu har da dansanda da kuma wani mahari a harin wanda aka kai a ginin majalisar dokokin.

Wata mata da ke tafiya a kasa na cikin mutanen da mota ta kade a kan gadar Westminster.

Haka kuma an caka wa wani dansanda wuka a majalisar dokokin ta Burtaniya da ke tsakiyar birnin London, kodayake an harbe maharin da ya caka masa wukar.

Akalla mutum 40 ne suka jikkata, cikin su har da 'yan sanda uku.

Firai Ministar kasar Theresa May za ta gudanar da taro kan tsaron kasar nan gaba kadan.

Hukumar tsaron ruwan birnin London ta ce an ceto wata mata daga kogin Thames, kuma ana ba ta kulawar gaggawa.

Firai Ministan Faransa Bernard Cazeneuve ya ce daliban kasar uku na cikin wadanda suka ji rauni sannan ya aike da sakon jaje da goyon baya ga Burtaniya.

Shugaban majalisar wakilai David Lidington ya shaida wa 'yan majalisar cewa "'yan sanda dauke da makamai sun harbe mutumin da ake zargi da kai harin".

'Yan majalisar sun ce sun ji harbin bindiga sau uku zuwa hudu. Wata majiya a fadar Firai Ministar Burtaniya ta ce babu abin da ya samu ita Firai Ministar Theresa May.

An ga lokacin da ake shigar da Theresa May ckin wata mota samfurin Jaguar a lokacin da ake harbe-harbe a cikin majalisar dokokin.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption 'Yan sanda sun harbe mutum daya

'An kaɗe mutane'

Wani ganau, Radoslaw Sikorski, ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Twitter wanda ya nuna mutanen da suka ji rauni kwance a kan titin Westminster Bridge.

Ya ce: "Yanzu wata mota ta kade mutum biyar."

Rundunar 'yan sandan kasar ta ce an kira ta domin magance harin da aka kai da makamai a kan gadar Westminster a yayin da aka raunata mutane da dama.

An dakatar da zirga-zirgar ababen hawa ta hanyar karkashin kasa da ke bi ta Westminster, sannan aka sauya wa motocin bas hanya.