'Rawar da BBC ta taka a rayuwata tsawon shekara 20'

Najwa
Image caption A yanzu haka Najwa tana hada digirin-digirgir dinta

Najwa Salisu Ahmad wata mai sauraron BBC ce tun tana karamar sakandare, kuma har yau ba ta daina ba, albarkacin cikar BBC Hausa shekara 60 da kafuwa, ta yi sharhi kan rawar da kafar ta taka a rayuwarta tsawon shekara 20.

Babban burin ko wane ma'aikacin jarida shi ne wane irin muhimmaci sakonnin da suke aika wa al'umma ke da shi a rayuwar mutanen. Wane tasiri sakon yake da shi, me aka fahimta, kwalliya tana biyan kudin sabulu?

Wadannan abubuwa su ne jigon tafiyar da aikin jarida har ma'aikatan ke samun kwarin gwiwar ci gaba da bayar da kaimi wurin aika sakonni.

Na fara sauraren sashen Hausa na BBC tun ina aji uku a sakandire, shekara kusan 20 da ta gabata kenan, saboda mahaifiyata ma'abociyar saurare ce.

Tun bana fahimtar me suke fada har na fara, daga nan kuma ya zamar mani jiki, wanda duk rana ta Allah ba ta wucewa ban saurari BBC Hausa ba, wanda a sanadiyyar haka ne har na fara sauraren sashen Turanci.

Hakika sauraron BBC ya taka muhimmayar rawa a rayuwata, ya sauya mani tunani da dama, musamman lokacin da na tsinci kaina a matsayin dalibar da ke koyon aikin jarida a jami'a, wanda kaunar BBC Hausan ce ma ta sani sha'awar karatun bangaren jaridar.

Akwai darasin da aka koyar da mu a jami'a na fannin 'ci gaban kasashen Afirka,' daya daga cikin aikin ajin shi ne kawo rahoto daga cikin shirin "Focus on Africa" shirin sashen Turanci na BBC, mafi yawan daliban a lokacin ba su san da wannan shiri ba, amma ni kasancewar ma'abociyar sauraren shirin ce, sai ya zamo mani abu mafi sauki.

Wannan yana daya daga cikin abubuwan BBC da ba zan iya mantawa dasu ba.

Misali lokacin da nake daliba mai sanin makamar aiki a gidan rediyon tarayya da ke Kaduna, na sha samun yabo kan yadda nake furta sunayen mutane Turawa da 'yan Kudu yayin gabatar da shirin "Siyasa Rigar 'Yanci," mamakinsu yadda nake furta sunayen, na kan ce duk lokacin da na saurari shirin sashen Hausa na BBC na fahimci cewa furta sunaye a cikin rahoto na kara wa rahoto armashi.

Image caption Najwa ta ce son sashen Hausa na BBC ne ya sa ta karanta aikin jarida a jami'ar Bayero

Abu na uku shi ne, shirin sashen Hausa ya taimaka mani na zama cikakkiyar masaniyar al'amuran yau da gobe, a duniya baki daya.

Duk abin da ke faruwa a duniya na kasance ina da ilminsa ta hanyar BBC, wani lokacin idan na bayar da bayanin abubuwan da na sani idan aka tambayeni, ina na samo ilmin, ni kaina sai na tsinci kaina da tambayar a ina na sami bayanin har ya zauna a kaina daram?

Na san ko tantama babu daga sashen Hausa na BBC ne.

'Jama'a na amfana da BBC'

Hakika BBC ta kasance uwa ma ba da mama wajen jagorantar duk wani gidan jarida da na sani a rayuwata. Ko shakka babu BBC ta karade duniya baki dayanta.

Misali, akwai littafin da na karanta na wani marubucin kasar Saudiyya mazaunin Jordan, Abdelrahman Munif, yana bayar da tarihin arzikin man fetur a kasar Saudiyya, har ya gangaro zuwan kayan fasahar zamani.

Da yazo batun rediyo, da BBC ya fara, inda ya jaddada muhimmancin gidan rediyon da irin rawar da suke takawa wajen fadakar da al'umma a duniya baki daya.

Na yi hira da mutane da dama kan muhimmancin da BBC ta taka a rayuwarsu, yayin da wasu su kan iya fada akwai wadanda suka ce muhimmancin sashen Hausa na BBC a rayuwarsu wani abu ne da ba zai iya misaltuwa ba.

Misali, akwai wacce ita ma ta ce min saboda sauraron sashen Hausa na BBC ne ta fara karatun koyon aikin jarida, inda a yanzu ta taka matsayin da mafarkinta bai taba gaya mata za ta taka a rayuwa ba.

A kwanan baya an yi wani muhimmin shiri kan "cutar sankara," wanda na san mata da dama da ya zaburar da su kan bukatar sanin me suke ciki da wannan mummunar cuta da yadda za su iya magance ta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Najwa na ganin ya kamata BBC ta kara kaimi kan shirye-shiryen da suka shafi mata

Rahotannin da suka fi burgeni

Cikin dubban rahotannin da na saurara, uku ne zan ce sun fi burgeni. Wadanda nake ganin alfanunsu ya sa dole a jinjina wa BBC.

Na farkonsu, ya faru ne a Kano, kan wani abu da ya saba ma al'adun Bahaushe da kuma addinin Islama, an yi rahotonne kan wata 'yar wasan Hausa da suka yi bidiyo na badala, wanda ya janyo ce-ce-ku-ce da dama.

Yayin da wasu ma basu yadda abun ya faru ba, kwatsam sai ga BBC ta sako hirarta da mutumin da abin ya shafa, wanda 'yan uwansa da duk wani na kusa da shi sun ba da tabbacin ba a san inda ya buya ba, iyalansa ma nemensa suke.

Babban abin burgewa a hirar shi ne yadda ya amsa laifinsa kuma ya nemi yafiyar Allah da ta al'umma. Tasirin da hirar ta yi shi ne tamkar BBC ta fesa wa kurar ruwa, ba ko jimawa zancen ya mutu mutane da dama suka nuna tun da mutum ya yi kuskure ya kuma amsa laifinsa ai ya cancanci yafiya.

Na biyu shi ne lokacin da aka rinka takaddama kan lafiyar marigayi tsohon Shugaban Nijeriya Umaru Musa Yar'adua. Yayin da wasu ke tabbatar da lafiyar shugaban, wasu kuma na ikirarin ai ba a raye yake ba, sai ga BBC ta sako muryar shugaban, inda ya tabbatar yana nan a raye.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ta ce BBC ta burge ta kan irin rahotannin da ta bayar lokacin da marigayi Shugaba Umaru 'Yar Adua ba shi da lafiya

Hakika wannan rahoton ma ya tasiri da magance al'amura da dama.

Na uku shi ne hirar da aka yi da uwar gidan Shugaba Muhammadu Buhari. Hirar ta dauki hankali sosai, saboda ta yi zantukan da suka janyo ce-ce-ku-ce kan siyasa da ba a taba samun matar shugaban kasar da ta yi irin su ba.

Jama'a sun tsammaci BBC za ta datse hirar ko ta rage abubuwan da ta fada, amma sai sashen Hausa ya yi aikin nasa, sai da ya gama tattaro hankalin jama'a tsab aka dawo kansa, ba tare da ta cire komai ba sai ta sako hirar. Wadannan rahotanni sun yi matukar burge ni.

Da dai a baya na fara korafi cewa BBC Hausa ta manta da sha'anin mata a shirye-shiryenta tun bayan shirin 'Haifi ki yaye'. Amma a bara na ce lallai da alama yanzu BBC ta tuno da mata bayan da ta shirya gasar rubutu ta mata zalla "Hikayata".

Zage dantse

A karshe ina kira ga sashen hausa na BBC da su kara kaimi wajen kasancewa kafar yada labaran da ba kamar ta.

Ina kuma so na yi kira da su fadada shirye-shiryen da suka shafi mata zalla, da za a rinka hira da matan da suka shahara ta hanyar ilmi ko ta sana'a, yayin da gwagwamaryar rayuwa bai sa sun yi kasa a gwiwa ba wajen cimma manufarsu, don zai taimaka mata su mike da neman ilmi da kuma na kansu.

Kuma ya kamata su kara bullo da shiri na musamman da za a rinka yi don mutanen karkara, watau fadakarwa kan illar almajiranci a arewa da nakasun da ke tattare da shi, tun da akasarin masu tura yara maza almajiranci suna kauyuka, hakazalika akasarin masu sauraren BBC na kauyuka.

Kazalika duk wadannan shirye-shirye baya ga yin su a rediyo, akwai kuma bukatar su dinga wallafa su a shafin intanet da shafukan sada zumuntarsu ganin cewa a yanzu nan hankalin mata da matasa ya fi karkata.

Labarai masu alaka