Kamfanin Twitter ya rufe shafukan 'yan ta'adda 377,000

Twitter
Image caption Kamfanin Twitter ya ce ya rufe shafukan mutane akalla 636,248 daga tsakiyar shekarar 2015.

Kamfanin Twitter ya ce ya rufe shafukan mutane akalla 636,248 daga tsakiyar shekarar 2015.

Kamfanin ya kara da cewa ya kulle kusan shafuka 377,000 na mutanen da ke rura wutar ta'addanci a karshen shekarar da ta gabata

An samu kari a kan shafukan da suka rufe na 'yan ta'adda gabanin wannan lokaci, ko da yake an maimaita sunayen wasu daga cikin shafukan kuma adadin zai iya fin haka.

Kamfanin dai na fuskantar matsin lamba domin tsayar da kungiyoyin ta'addanci irin su IS daga amfani da shi.

Ko a shekarar da ta gabata ma Majalisar Tarayyar Turai ta ce shafin ya zama "wata kafa" ta yada tsattsaurar akida a shafin intanet

A rahoton kamfanin na baya-bayan nan, wanda ya fara daga daya ga watan Yuli, zuwa 31 ga watan Disambar bara, ya ce an inganta matakai domin magance matsalar.

Ya ce kashi 74 cikin 100 na shafukan da aka rufe an same su ne saboda samun su da laifi da hukumar da ke kula da shafin ya yi.

Ya kuma ce ya rufe jumlar shafuka 636,248 da ke rura wutar ta'addanci, tun watan Agustan 2015, lokacin da aka fara bincikar lambobin

'Yaduwar tashin hankali'

A watan Agustan bara ne, kwamitin harkokin cikin gida na Birtaniya ya zargi kamfanonin Twitter da Facebook da kuma YouTube, da cewa sun kasa tabuka wani abin a-zo-a-gani wajen tsayar da yaduwar ta'addanci da kuma tsauraran akidu a shafukansu.

Kuma 'yan majalisar dokoki sun ce Twitter ya zama wani dandali na yaduwar ta'addanci, kuma shafukan da kamfanin ya rufe ba su taka-kara-suka karya ba.

Farfesa Tahir Abbas, wani babban mai bincike ne a cibiyar Think tank Rusi, ya bayyana wa BBC cewa, "Shafin Twitter wani babban makami ne da ke hannun wadanda ke son sanya tsoro da kuma kiyayya, kuma yake tara mutane tare da ba su damar shiga aikin ta'addanci."

"Amma yana da kyau a san cewa kokari da kuma nasarorin da ake samu na kara inganta gyaruwar abubuwa."

Ya kara da cewa, "Wannan yana da matukar muhimmanci, kuma a fili yake cewa idan akwai shafuka da yawa, akwai yiyuwar samunsu a ko'ina."

Labarai masu alaka