Rigakafin Rotavirus zai iya ceton yara 500,000

jinjiri Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hukumar lafiya ta duniya, ta ce sama da yara 500,000 ne ke mutuwa duk shekara sakamakon rashin isashen ruwa a jiki

Ana da kwarin gwiwa a kan wani sabon rigakafi da zai iya kare yara daga cutar da ke kashe yara 1,300 kullum bayan da aka yi wani gwaji a jamhuriyyar Nijar.

An gano cewa rigakafin zai iya kare yara daga cutar amai da guduwa wadda kwayar cutar Rotavirus ke haddasawa da kashi 67 cikin 100.

Rigakafin guda biyu na bukatar a saka su cikin firji kuma yana da tsada sosai.

Za a sayar da sabon maganin rigakafin a rabin farashinsu.

Daraktar Kungiyar likitoci ta Medicins Sans Frontieres, Micaela Serafini, ta bayyana rigakafin wanda ake kira BRV-PV a matsayin wani abu da "ya kawo sauyi".

Ta shaida wa gidauniyar Thomson Reuters cewa, "Rigakafi ne da ya dace da abin da muka yi amanna ya fi ma abin da Afirka ke bukata.

A cewar hukumar lafiya ta duniya, sama da yara 500,000 ne ke mutuwa duk shekara sakamakon rashin isashen ruwa a jiki da kuma cututtukan da suke da alaka da kwayar cutar Rotavirus, musamman a yankin kudu da hamadar Sahara.

Amma rigakafin na baya-bayan nan na da wahalar a yi safarasa kuma a bai wa yara saboda yana bukatar ya kasance cikin firinji a ko wanne lokaci.

Sai dai da wuya ragakafin da ke da bukatar a saka shi a firji iya kai wa ga yaran da ke karkara.

Wani malami a jami'ar Havard ya ce, "Idan rigakafin ya wadata a Afirka, zai kare miliyoyin yara da ka iya kamuwa da cutar."

Rigakafin BRV-PV, wanda ake samarwa a Indiya, na bukatar amincewa daga wajen hukumar lafiya ta duniya kafin a fara amfani da shi a duniya baki daya.

Labarai masu alaka