An sallami Hosni Mubarak daga gidan yari bayan shekara shida

Hosni Mubarak (April 2016) Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An zargi Mubarak da kisan masu zanga-zanga

An sallami tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak daga gidan yari, shekara shida bayan an tumbuke shi daga mulki sakamakon boren da 'yan kasar suka yi.

Lauyan Mr Mubarak ya ce tsohon shugaban kasar ya bar asibitin soji da ke kudancin birnin Alkahira inda ya tafi gidansa da ke garin Heliopolis da ke arewacin kasar.

Wata kotun daukaka karar kasar ce ta bukaci a sallame shi a farkon watan da muke ciki bayan ta wanke shi daga zargin kisan masu zanga-zanga a lokacin boren shekarar 2011.

Mista Mubarak, mai shekara 88, ya zama shugaban kasar Masar a shekarar 1981 bayan kisan gillar da aka yi wa Anwar Sadat.

Tun a shekarar 2013 ake tsare da shi a asibitin soji da ke Maadi, bayan an kai shi can daga gidan yarin Torah a matsayin beli.

'Ba a son sakinsa'

A shekarar 2012 ne aka yanke wa Mr Mubarak hukuncin daurin rai-da-rai saboda samun sa da hannu wurin kisan masu zanga-zanga, wadanda suka mutu a hannun jami'an tsato a watan fabrairun 2011.

Sai dai an sake yi masa shari'a inda a watan Mayun 2015 wani alkali ya bayar da umarnin sakin Mr Mubarak daga gidan kaso.

Sai dai rahotanni na cewa gwamnatin Abdul Fattah al-Sisi ba ta son sakinsa saboda matsalar da hakan ka iya janyo wa daga wurin 'yan kasar.

Mr Sisi ya taba yin aiki a matsayin shugaban hukumar leken asiri karkashin mulkin Mr Mubarak, kuma shi ne ya jagoranci juyin mulkin da aka yi wa magajin Mubarak, Mohammed Morsi a 2013.

An yi amannanar cewa fiye da mutum 800 ne suka mutu lokacin da jami'an tsaro suka yi taho-mu-gama da masu zanga-zanga a biranen Alkahira, Alexandria, Suez da wasu biranen kasar, inda aka kwashe kwana 18 ana boren ganin bayan Mr Mubarak.

Labarai masu alaka