Gwamnatin Gambia za ta binciki Yahya Jammeh

Yahya Jammeh Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yahya Jammeh ya yi juyin mulki a 1994

Ministan sharia'ar Gambia ya ce za a kafa wani kwamitin Gaskiya da Sasantawa domin ya yi bincike kan cin zarafin da aka aikata a lokacin mulkin tsohon Shugaba Yahya Jammeh.

Minista Abubacarr Tambadou ya kara da cewa za kuma a gudanar da bincike kan dukiyar da tsohon shugaban kasar ya tara.

A cewarsa, za a bukaci mutanen da suka ci zarafin wasu 'yan kasar da su fadi hakan, sannan a nemi wadanda lamarin ya shafa su yi musu afuwa.

An zargi tsohuwar gwamnatin Mr Jammeh, wanda ya shafe sheka 22 a kan mulki, da cin zarfin jama'a, ciki har da gallazawa da batar da su.

Haka kuma an yi zargin cewa kimanin $11m sun yi batan-dabo daga bautul malin Gambia lokacin da Mr Jammeh ke ficewa daga kasar a watan Janairu.

Ya fice ne zuwa Equatorial Guinea bayan dakarun kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma sun shiga Gambia da zummar tilasta masa mika mulki ga mutumin da ya lashe zaben kasar Adama Barrow.

Wata sanarwa da Mr Tambadou ya fitar ta ce, "Za a kafa kwamitin Gaskiya da Sasantawa nan da wata shida masu zuwa kuma za a soma sauraren ba'asin jama'a daga nan zuwa karshen shekara."

A watan Janairu ne aka tsare tsohon shugaban hukumar leken asirin Gambia Yankuba Badjie, inda ya zama babban jami'in tsaron gwamnatin Mr Jammeh na farko da sabuwar gwamnatin kasar ta kama.

Har yanzu dai ba a fadi dalilin kama shi ba.

Mr Barrow ya ce gwamnatinsa ba za ta mayar da hankali wajen ramuwar gayya ba, yana mai cewa a maimakon hakan za ta kafa kwamitin Gaskiya da Sasantawa.