Nigeria da Senegal sun yi canjaras

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Dan Mullan
Image caption Super Eagles sun kara da Teregon Lions

Najeriya da Senegal sun tashi 1-1 a wasan sada zumuntar da suka yi da yammacin Alahamis, a filin wasa na Hive Stadium da ke birnin Landan.

Dan wasan Senegal, Moussa Sow ne daai ya fara zura wa Najeriya kwallo bayan hutun rabin lokaci, kafin daga bisani Kelechi Iheanacho ya farke wa Najeriyar ta hanyar bugun fanaret, a minti 10 karshe.

Victor Moses da Carl Ikeme dai ba su buga wasan ba sakamakon rauni amma dan wasan Liverpool, Saido Mane ya buga wa kungiyar Teranga Lions ta Senegal.

Wasan da Najeriya za ta buga nan gaba a filin wasan na Hive shi ne karo da urkina Faso.