Nigeria: An dakatar da wani Basarake saboda 'fyade'

Rawanin wani Basarake a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yawan samun labarin aikata fyade a Najeriya

Majalisar masarautar Katsina ta dakatar da Bashir Bala Kofar-bai daga mukaminsa na 'Magatakarda' saboda zargin aikata laifin fyade da ake yi masa.

Sakataren Majalisar masarautar, Bello Ifo, ya fada a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, cewa dakatarwar ta fara aiki ne nan take.

Bashir Bala na fuskantar shari'ar aikata laifin fyade ga wata yarinya 'yar shekara 15 makonni biyu da suka gabata a Katsina.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa ana zargin Basaraken ne da yi wa yarinyar fyade, bayan da mahaifinta wanda ke aiki a karkashin Basaraken ya aiketa gidansa.

Yarinyar ta sanar da iyayenta halin da take ciki, inda suka dauke ta zuwa asibiti domin duba lafiyarta.

Daga nan kuma iyayen suka sanar da 'yan sanda, inda aka kama shi tare da tsare shi domin gudanar da bincike.

Hadin gwiwwar kungiyoyin fararen hula a Jahar dai, na kara matsa wa 'yan sanda lamba, da su tabbatar da adalci a kan lamarin.

Batun aikata fyade ga kananan yara na ci gaba da addabar al'umma musamman a arewacin Najeriya.

A lokuta da dama akan zargi hukumomi da kasa yin katabus wurin hukunta wadanda ake zargi.

Labarai masu alaka