An haramta wa dan kwallon Tottenham Dele Alli buga wasa uku

Dele Alli Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kori Alli a minti na 39 a wasansu da Gent lokacin da aka fitar da Tottenham din

An haramta wa dan wasan tsakiya na Tottenham Dele Alli wasannin Turai uku bayan da aka kore shi a karawarsu da Gent, a filin wasa na Wembly a wasan Europa da suka buga a watan Fabrairu.

An kori Alli ne dai saboda ya kalubalanci Brecht Dejaegere a wasan da suka tashi kunnen-doki 2-2

A kokarin da kungiyar ke yi na zama ukun farko a gasar firimiyar bana, Alli dai zai rasa rabin wasannin da suka saura a gasar.

An ci tarar Arsenal £4,300 bayan wasu daga cikin magoya bayan kungiyar sun rika gudu a kan layin filin wasa lokacin da Bayern Munich ta doke su 5-1 a gidansu.

Haka kuma Uefa ta ci tarar Bayern Munich £2,600 bayan da magoya bayan kungiyar suka yi ta jefa takardu cikin filin wasan Arsenal saboda tsadar kudin tikiti.

Ita ma kungiyar Saint-Etienne na fuskantar tarar £43,000 bayan da magoya bayanta suka yi ta jefa abubuwa cikin filin wasa lokacin wasansu na Europa da Manchester United a filin wasa na Old Trafford a watan da ya gabata.

Tottenham din, wacce Gent ta fitar daga gasar Europa , tana matsayi na biyu a kan teburin firimiya, kuma saura wasa 10 a kammala gasar.

An dai haramta wa Alli wasanni uku a kakar wasannin firimiyar bara, saboda samunsa da laifin dukan dan wasan West Brom Claudio Yacob.

Labarai masu alaka