ICC za ta ba da diyya ga mutanen da rikicin DR Congo ya shafa

DR Congo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yanke wa Katanga hukunci a shekara 2014 inda yake gidan yari a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Kotun hukunta mayan laifuka ta duniya a Hague na shirin yanke hukunci na farko a kan kuɗaɗen da za a bai wa waɗanda yaƙi a DR Congo ya shafa.

Hukuncin na ba da kuɗaɗe zai taimakawa mutane fiye da 300 wadanda laifin yaki ya shafa a shekara 2003 a Jamhuriyar Dimokradiyyar ta Congo.

Lauyoyin wadanda abin ya shafa sun bayyana jerin asarar da mutanen suka yi da suka hada da ta gidaje da kujeru da shanu da kajin da aka kashe musu da kuma tashin hankalin da suka shiga a sakamakon mutuwar 'yan uwansu.

Za su karbi diyyar da ta kai fiye da dalar Amurka miliyan uku, inda kowannensu zai samu dala 250.

A halin yanzu Germain Katanga na zaman kurkuku bayan an yanke masa hukunci na shekara 12 saboda samunsa da aikata laifukan yaki.

Kuma yana kallon yadda zaman kotun yake wakana kai tsaye daga dakin tsare masu laifuka na gidan jarun da ke birnin Kinshasa.

An dai bukaci Mr. Katanga ya biya diyyar dala miliyan daya.

Alkalin kotun, Marc Perrin de Brichambaut ne ya sanar da adadin kudaden da Mr. Katanga zai biya ga mutanen kauyen Bogoro da harin ya shafa.

Bayan la'akari da duk abubuwan da aka zayyana, kotun ta kididdige diyyar da Mr. Katanga zai biya a kan dala miliyan daya bisa ka'idan daidai ruwa daidai tsaki.

Idan kuma Madugun 'yan tawayen ba zai iya biyan diyyar ba, za a debi kudaden ne daga wani asusu na kotun wanda ke samun tallafi daga kasashe mambobin kotun.

Kotun hukunta manyan laifukan yakin ta duniya ta sha fuskantar suka daga kungiyar tarayyar Afrika da kuma wasu kungiyoyin daban bisa yin shari'un da galibinsu sun shafi shugabannin kasashen Afrika ne.

Wannan diyyar dai na kara karfafa kokawar da masu shigar da kara suka ce kotun na yi domin tabbatar da adalci ga mutanen da aka cutar.

Daraktan asusun ya bayyana cewa abu ne mai muhimmanci a nuna cewa tabbatar da adalci bai tsaya kawai a cikin kotu ba.