Kun san Khalid Masood, mutumin da ya kai harin Landan?

Hoton Khalid Masood ; wanda ya kai harin Landan.
Image caption Khalid Masood , mutumin da ya kai harin Landan.

Wani jami'in dan sanda ya ce an tabbatar da Khalid Masood, mai shekara 52 ne ya kai harin Westminster.

Dan sandan ya ce sunansa na haihuwa shi ne Adrian Russell Ajao, daga bisani ya musulinta sunansa ya koma Khalid Masood.

An haife shi ne a garin Kent yanzu kuma yana zaune a yammacin Midlands.

Masood yana da 'ya'ya uku.

Har wa yau, an tabbatar da ya zauna a garin Crawley, da yammacin Sussex, da Rye, da Eastbourne, duk suna yankin East Sussex, da Luton da kuma gabashin Landan a lokuta daban-daban.

An yi masa takardar haihuwa a gundumar Dartford ta garin Kent, da sunan Adrian Russell Elms, bayan wasu makonni da haihuwarsa a ranar Kirsimati na shekarar 1964.

Elms shi ne sunan mahaifiyarsa na farko, amma bayan haihuwarsa da shekara biyu ta auri wani mutum mai suna Ajao.

Kafin ya kai harin yana canje-canjen sunan mahaifi kafin ya musulunta ya koma Massod.

Mahaifiyarsa da mijinta sun zauna a garin Tunbridge Wells, da Kent, na tsawon lokaci, kafin su koma Wales.

'Yan sandan-ciki na hukumar yaki da ta'addanci na shiyyar Wales sun bincike gidansu, amma ba a samu wani a cikinsu a matsayin wanda ake zargi ba.

'Yan sanda sun bayyana cewa Masood sananne ne a wurinsu, domin a baya ma an sha samunsa da aikata laifuka, da suka hada da tayar-da-zaune-tsaye.

Masood ya amsa laifinsa na farko yana dan shekara 19, a watan Nuwambar shekarar 1983 a matsayin mai aikata babban laifi.

A shekarar 2000 ne, lokacin yana zaune a garin Northiam kusa da Rye a garin Kent, daga nan aka yankewa Adrian Elms hukuncin daurin shekara biyu bayan ya amince da kai wa wani mutum hari da wuka a wata mashaya.

Khalid Masood ya kai hari Wentminsta da ke Landan a ranar Laraba.

Daga cikin mutam hudun da abun ya rutsa da su akwai mai suna, Leslie Rhodes mai shekara 75 daga garin Streatham a kudancin London daya daga cikin mutum ukun da motar Masood ta hallaka a kan gadar Westminster.

Sa'annan kuma Masood ya daba wa dan sanda Keith Palmer wuka a kusa da fadar 'yan Majalisun. 'Yan sandan sun ce sun sake kama mutum biyu.

Mutum 50 ne suka jikkata a harin, da wasu mutum 30 da ake ba su kulawa a asibiti,biyu na cikin mawuyacin hali, daya kuma na halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai.

Yayin da yake karin bayani a kofar ofishin mataimakin Kwamishina Mark Rowley a kasar New Scotland Yard, ya ce jami'an 'yan sanda biyu na asibiti cikin rauni mai tsanani.

Labarai masu alaka