Nigeria: Babu shakka digirina takwas — Dino Melaye

Sanata Dino Melaye Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Sanata Dino Melaye ya ce yana takardun shaidar duka digirin da ya yi

Dan majalisar dattawan Najeriya, sanata Dino Melaye ya ce tabbas yana da shaidun digiri takwas din da ake zargi bai yi ba.

Jaridar da ake wallafawa a shafin intanet ta Saharareporters ne dai ta wallafa wani labari da ke nuna cewa makarantar horo kan tattalin arziki da ke birnin London ta karyata digirin da Dino Melaye ya ce ya yi a can.

Wannan ne kuma har ya janyo Sanata Dino ya kai kamfanin jaridar kara.

A makon da ya gabata ne kuma tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar ta dattawa, sanata Ali Ndume ya nemi majalisar da ta yi bincike kan zargin da aka yi wa Dino Melaye na rashin kammala jami'a.

To amma a wata hira da Ibrahim Isa, Dino ya ce duk wanda yake tababar mallakar digiri to ya fito da shaidar da ke nuna hakan.

Dino Melaye ya kuma yi tsokaci kan kin amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC ta kasar.

Ku saurari yadda hirar ta kaya:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Sanata Dino Melaye