Dakarun Amurka sun kashe fararen hula da dama a Iraqi

Iraqi Mosul Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dubban mazauna birnin Mosul ne suke tsere daga yankunan da ake kai hare-hare ta sama

Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta tabbatar da cewa wani jirgin yakin dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta ya kai hari tare da hallaka fararen hulla da dama cikin yankin gabashin Mosul da mayakan IS ke iko shi a Iraƙi.

Wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta fitar, ta ce ta fara gudanar da bincike kan hari ta sama da aka kai a cikin makon da ya gabata.

Mazauna yankin sun ba da rahoton cewa an zaƙulo gawa 50 daga cikin gine-gine, yayin da ake kyautata zaton buraguzai sun binne wasu mutanen da dama.

Yanzu haka an bayyana cewa dubban mazauna birnin na Mosul sun tsere daga yankunan da ke hannun mayakan IS, don fargabar hare-hare ta sama da dakarun da Amurka ke jagoranta ke kai wa, baya ga ƙazamin fadan da ake gwabzawa da dakarun Iraqi ta kasa.

Ana kuma iya ganin hayaki ya turnuke sama a yankin, yayin da jiragen yaƙi ke ci gaba da luguden wuta a ranar Asabar.

Image caption Mazauna yankin sun ce mayakan IS na yi garkuwa da fararen hula

Mazauna yankin sun ce mayakan na IS na amfani da fararen hula a matsayin garkuwa, inda suke boyewa cikin gidaje tare da tilasata wa matasa shiga fagen dagar.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan ainihin abin da ya faru, amma wasu rahotanni na cewa hare-haren sun hallaka mutane fiye da 100.

Muddin hakan ta tabbata zai kasance mutuwar fararen hula mafi munin da aka taba samu a hare-hare ta saman da Amurka ke jagoranta tun daga shekara ta 2003.

A kasar Syria makwabciyar Iraqin inda a can ma dakarun kawance ke fafatawa da mayakan na IS, mutane akalla 33 ne aka hallaka a farkon wannnan makon.

Image caption Hare-hare ta sama sun lalata kusan daukacin tsohon birnin Mosul

Mataimakin shugaban kasar Iraqi Osama al-Nujaifi ya ce wani babban bala'in da ya shafi bil'adama ne ke faruwa sakamakon amfani da karfin soji, yayin da dakaru masu goyon bayan gwamnati ke kokarin fatattakar masu tada kayar baya daga birnin Mosul.

Yayin da yake magana a birnin Amman na kasar Jordan, mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniya WHO, Altaf Musani, ya ce fararen hula na fuskantar barazanar halaka su ko kuma jikkatawa.

''Fararen hula na kara fadawa cikin barazana saboda hare-hare ta sama, adadin wadanda za su mutu ko kuma jikkata ka iya ƙaruwa.''

Majalisar Dinkin Duniya ta kadu game da asarar rayukan da aka yi , in ji jami'ar tsare-tsarenta kan ba da agajin jin-kai a kasar Iraqi Lise Grande.

Labarai masu alaka