'Shan gishiri na kawo fitsarin dare'

Likitoci sun ce rage shan gishiri na ingata rayuwa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Likitoci sun ce rage shan gishiri na ingata rayuwa

Likitoci a kasar Japan sun bukaci mutanen da ke yawan tashi da daddare domin yin fitsari da su rage shan gishiri a abinci idan suna so su daina yawan tashi.

Matsalar yawan tashin fitsarin dare - wacce ta fi addabar mutanen da suka haura shekara 60, tana hana mutum samun bacci mai dadi sannan tana yin illa ga rayuwar mutanen.

Wani bincike da likitoci suka gudanar kan mutum 300, ya gano cewa rage shan gishiri a abinci yana sanya wa mutane su rage yawan tashi yin fitsarin dare.

Likitocin na Jami'ar Nagasaki sun fitar da sakamakon bincikensu ne a wurin taro na kungiyar kula da mafitsara ta Turai da aka yi a Landan.

Sun bibiyi mutanen da ke shan gishiri sosai da kuma matsalar rashin bacci tsawon wata uku, bayan sun ba su shawara su rage shan gishirin.

Binciken ya nuna cewa sun rage zuwa fitsarin dare daga sau biyu zuwa sau daya.

Baya ga haka, binciken ya nuna cewa mutanen da suka rage shan gishirin da rana ma sun daina yawan zuwa fitsar sannan rayuwarsu ta inganta.

Matsalar yawan tashi yin fitsari da daddare ta fi samun mutane - maza da mata- da suka manyanta.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yawan gishiri na da illa a jiki

Labarai masu alaka