An kai hari a wani gidan rawar Amurka

'Yan sanda Cincinnati sun ce harin ya yi muni Hakkin mallakar hoto CPD
Image caption 'Yan sanda Cincinnati sun ce harin ya yi muni

'Yan sanda a Amurka sun ce akalla mutum daya ne ya mutu kana mutum 14 suka jikkata sakamakon harin bindigar da aka kai a wani gidan rawa da ke birnin Cincinnati na jihar Ohio.

'Yan sandan sun ce 'yan bindiga biyu ne suka kai harin a gidan rawar na Cameo.

Wani mataimakin shugaban 'yan sanda Paul Neudigate ya shaida wa gidan talabijin na WLWT-TV cewa mutane da dama sun samu raunuka masu tsanani.

Mr Neudigate ya ce, "Muna tsaka da fuskantar babban bala'i a gidan rawar inda lamarin ya shafi mutane da dama."

Wata jami'ar 'yan sanda Kimberly Williams ta ce 'yan bindigar sun tsere kuma ba a da cikakken bayani a kansu.

Ta kara da cewa ganau ba sa son ba su hadin kai kan batun.

Williams ta ce, "A wannan mataki ba a san abin da ya sa suka kai harin ba. Sai dai mun yi amannar 'yan bindigar da suka kai harin suna da yawa."

Wannan lamari ya faru ne kusan shekara guda bayan wani dan bindiga Omar Mateen ya bude wuta kan wani gidan rawa da 'yan luwadi ke taruwa a birnin Orlando na Florida.

Mateen ya kashe mutum 49 a harin da ake ganin daya daga cikin mafiya muni da aka kai Amurka.

Labarai masu alaka