'Bai kamata WhatsApp ya zama mafakar 'yan ta'adda ba'

Amber Rudd Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Amber Rudd ta ce za ta yi taro da shugabannin shafukan zumunta

Ministar harkokin gidan Burtaniya ta ce dole ne kamfanonin shafukan zumunta su bai wa jami'an tsaro damar yin kutse cikin sakonnin da ake tura wa ta shafukansu domin hana 'yan ta'adda yin amfani da su wurin kai hare-hare.

Amber Rudd ta ce "Bai kamata a samar wa 'yan ta'adda mafaka ba."

An fahimci cewa mutumin da ya kai harin Landan Khalid Masood, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum hudu, ya yi amfani da manhajar WhatsApp minti biyu kafin ya kai harin.

Ministar ta ce za ta gana da kamfanonin shafukan zumunta na zamani a wannan makon domin su yi aiki tare.

Shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn ya ce ai dama hukumomi suna da dama mai karfi ta sanin sirrin da ke cikin shafukan zumunta.

Ms Rudd ta shaida wa BBC cewa: "Ba za mu taba amincewa da boye-boyen da shafukan zumunta ke yi ba. Bai kamata a bai wa 'yan ta'adda mafaka ba."

Ta kara da cewa: "Akwai bukatar sanin abubuwan da shafuka irin su WhatsApp ke yi, don haka bai kamata a bai wa 'yan ta'adda wani dandali da za su rika ganawa da juna ba."

A cewar ta, ya kamata jami'an tsaro su samu damar warware dukkan kullun da ke cikin sakonnin da ake aikawa.

A halin da ake ciki dai jami'an tsaro ba sa iya kutsawa cikin sakonnin da ake aikawa ta manhajar WhatsApp.

Image caption Sunan Masood na farko shi ne Adrian Elms

Shafin Facebook, wanda ke da mabiya sama da biliyan daya, ya ce kare sakonnin da masu amfani da shi ke aikawa na cikin "ginshikan kafa" kamfanin.

Shi ma mai kamfanin Apple Tim Cook ya ce bai kamata gwamnati ta tilasta wa kamfaninsa mika mata bayanan sirrin masu amfani da shi ba.

Sai dai Ms Rudd ta ce: "Ina ganin akwai bukatar mu gaya wa Tim Cook ya sake tunani kan hanyar da zai taimaka mana idan matsala irin wannan ta taso."

Hakkin mallakar hoto PA/Facebook
Image caption PC Keith Palmer, Kurt Cochran da Aysha Frade na cikin wadanda suka mutu sakamakon harin Landan

Labarai masu alaka