Kifewar kwale-kwale ta janyo wa wasu ɗauri a Masar

Wadanda suka tsira sun ce an makare kwale-kwalen da mutane Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadanda suka tsira sun ce an makare kwale-kwalen da mutane

Wata kotu a Masar ta yanke wa mutum 56 hukuncin dauri saboda samunsu da hannu a kifewar da wani kwale-kwale ya yi a watan Satumba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 200.

An yanke wa mutanen hukuncin daurin shekara 14 bayan an same su da laifin kisan kai da yin sakaci.

Kwale-kwalen na kan hanyarsa ta zuwa Italiya ne lokacin da ya kife a nisan kilimita 12 daga tekun da ke birnin Rosetta da ke gabar teku.

An yi kiyasin cewa kusan mutum 450 ne a cikin kwale-kwalen, cikin su har da kusan mutum 100 da aka sanya a wurin zaman direba.

Mutum 163 suka tsira daga kwale-kwalen, kuma akasarinsu 'yan kasar ta Masar ne.

Akwai 'yan kasashen gudu hijirar Syria da Eritrea da kuma Somalia a cikin kwale-kwalen.

Labarai masu alaka