An kashe ma'aikatan agaji da dama a Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kashe ma'aikatan agaji da dama a Sudan ta Kudu yayin da suke fafutuka kan karancin abincin da tashin hankali ya haifar

Ma'aikatan agaji shida ne aka yi wa kwanton bauna ranar Asabar tare da hallaka su yayin da suke kan hanyar zuwa garin Pibor daga Juba babban birnin kasar.

Wannan shi ne hari irinsa na uku a cikin wata guda, ko da shi ne mafi muni ta fuskar yawan asarar rayuka lokaci guda, tun bayan fara rikicin Sudan ta Kudu a shekara ta 2013.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da wannan kisa.

Sudan ta Kudu na cikin halin tsaka mai wuya sakamakon tashe-tashen hankula bayan shafe sama da shekara uku ana tafka yakin basasa.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ma'aikatan agaji 12 aka hallaka a cikin wannan shekara, yayin da kungiyoyin ba da agaji ke ta fafutuka kan karancin abincin wanda tashin hankali ya haddasa.

Ta ku,a ce ma'aikatan agajin akalla 79 ne aka hallaka a Sudan ta Kudu tun bayan fara rikici a cikin watan Disamban 2013.

A ranar 14 ga watan Mayu ne kuma aka kai hari kan ayarin motocin agaji yayin da suke kai dauki a garin Yirol na gabashin kasar, inda aka samu barkewar annobar kwalara, inda aka hallaka ma'aikacin agaji da wani maras lafiya.

Haka kuma, wasu 'yan tada-kayar-baya sun tsare wani ma'aikacin wata kungiya ta kasan duniya a ranar 10 ga watan Maris, yayin wani fada da ya barke a garin Mayendit tsawon kwana hudu kafin su sako shi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sudan ta Kudu ta fada cikin tashin hankali tun bayan fara yakin basasa shekaru 3 da suka gabata

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana cewa wasu yankunan Sudan ta Kudu sun fada cikin ja'ibar yunwa, kuma mutane kusan miliyan bakwai da rabi ne ke bukatar agajin jin-kai.

Tashin hankali mai nasaba da kabilanci ya mamaye Sudan ta Kudu wadda ta samu 'yancin kai a shekara ta 2011.

An fara yakin basasa kuma bayan takun-sakar da ta faru tsakanin shugaba Salva Kiir dan kabilar Dinka, da tsohon mataimakinsa Riek Machar dan kabilar Nuer.

A ranar Alhamis ne dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya suka bai wa fararen hula kusan dubu daya kariya a garin Pibor, a bisa fargabar yiwuwar kai musu farmaki, bayan arangamar da aka yi tsakanin bangarorin kabilun biyu.

Labarai masu alaka