An haramtawa 'yan matan da suka yi ciki zuwa makaranta a Saliyo

Hawa studies hairdressing Hakkin mallakar hoto Olivia Acland

An haramtawa 'yan matan da suka yi ciki zuwa makaranta a kasar Saliyo, domin ana ganin idan aka bar su suka ci gaba da zuwa, to za su koyawa sauran dalibai munanan dabi'unsu.

A watan Afrilun shekarar 2015 ne aka sake bude makarantun kasar, bayan da aka yi fama da annobar cutar Ebola.

Ma'aikatar ilimin Kimiyya da fasaha ce ta bayar da sanarwar haramtawa 'yan matan da suka yi ciki zuwa makaranta da kuma zaunawa jarabawa.

An sanya haramcin zuwa makarantar ne ta hanyar yi wa 'yanmatan binciken kwakwaf.

Luci is pregnant with her second child Hakkin mallakar hoto Olivia Acland

Kasa da shekara biyu kenan da sanya haramcin, amma har yanzu ba a janye dokar ba.

Yanzu haka dai cibiyoyin koyar da sana'o'i da suka kware a fannonin da suka hada da koyar da girke-girke da dinki, da gyaran gashi su ne suka maye gurbin makaranta a wurin 'yan matan da suka yi cikin.

Olivia Acland ne ya dauki hotunan wadannan 'yan matan, suka kuma ba shi labaransu, inda ya gano cewa da matukar wuya ka ga irin wadannan 'yan mata sun koma makaranta don ci gaba da karatu bayan an kore su.

Emma sits with a small child Hakkin mallakar hoto Olivia Acland

Emma 'yar shekara 20 ta ce, "Lokacin da na yi ciki ne na koma cibiyar koyan sana'o'i, inda anan ne na koyi sana'ar girke-girke. A lokacin da nake makaranta dole ce ta sa na gayawa malamarmu cewa ina dauke da juna-biyu sakamakon kama ni da ta yi ina bacci a aji. Daga nan ne ta ja ni zuwa ofishin shugabar makarantar, aka kuma ce mini cewa kar na sake dawowa".

Mariema stands against a wall Hakkin mallakar hoto Olivia Acland
Isatu stands outside Hakkin mallakar hoto Olivia Acland

Isatu 'yar shekara 18 wadda take so ta zama mai yin gyaran gashi, ta ce: "Ina koyon sana'a a cibiyar koyar da sana'o'i da ke kusa da inda nake. Na ci burin zama likita, amma ba na tunanin burina zai cika a yanzu. Ina shakkar ba zan kara komawa makaranta ba".

Zainab stands outside Hakkin mallakar hoto Olivia Acland
Jeneba stands outside Hakkin mallakar hoto Olivia Acland

Jeneba ta ce, "Na tuna abin da shugabar makarantarmu ta ke cewa, abin kunya ne ga makarantar da aka samu 'yan matan da suka yi ciki su ci gaba zuwa."

"A lokacin da cikina ya fara fitowa, sai na daina zuwa makaranta. Duk lokacin da naga kawayena sun saka kayan makarantarsu sai na ji kunya da bakin-ciki sun kama ni," in ji ta.

Isha sits on the sofa Hakkin mallakar hoto Olivia Acland

Photographs taken by Olivia Acland

Labarai masu alaka