Me ya sa Buhari ya fasa zuwa Sambisa?

Burutai
Image caption An shirya shugaba Buhari da babban hafsan sojin kasar Laftana Janar Yusuf Tukur Burutai ne za su kai ziyarar da farko

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soke ziyarar da ya shirya kai wa dajin Sambisa, inda nan ce maboyar kungiyar Boko Haram.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ne ya tabbatar da hakan, amma bai bayar da cikakken dalili na soke ziyarar ba.

Amma wasu na ganin dalilai na tsaro ne suka sa aka soke ziyarar.

Mista Adesina ya ce ministan tsaron kasar Mansur Dan Ali ne, zai wakilci shugaban kasar yayin ziyarar.

Tun farko dai an shirya cewa shugaba Buharin da babban hafsan sojin kasar Laftana Janar Yusuf Tukur Burutai ne za su ziyarci dajin Sambisan a ranar Litinin 27 ga watan Maris, domin bikin gasar harbi da sojojin kasar za su yi.

Sojojin kuma za su yi amfani da wannan damar domin rarraba magunguna da kayan agaji ga 'yan gudun hijirar da ke zaune a sansanonin Bama da Kondiga da kuma Magumeri da ke jihar Borno.

Sannan kuma za su tattauna da sarakunan gargajiya na yankin, a kan al'amuran da suka shafi tsaro.

A watan Disambar bara ne dai sojojin kasar suka samu nasarar fatattakar mayakan Boko haram daga maboyarsu ta karshe a dajin Sambisa.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a watan Disambar, shugaba Buhari ya ce mayakan kungiyar suna kan arcewa ne, kuma ba su da sauran wurin buya.

Sai dai kuma duk da ikirarin da sojoji suke yi na cewa suna samun galaba a kan kungiyar, a baya-bayan nan ana samun karuwar hare-haren kunar bakin wake a jihar Bornon.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da shugaba Buhari ya soke zuwa wata ziyara wani yankin kasar ba.

A watan Yunin 2016 ma shugaban ya soke ziyarar da aka shirya zai kai yankin Naija Delta domin kaddamar da shirin share man da ke malala a yankin.

Babu wata hujja da aka bayar ta soke ziyarar, sai dai wasu majiyoyi na cewa hare-haren da masu tayar da kayar baya ke kaiwa ne suka hana shi zuwa.

Labarai masu alaka