Nigeria: CBN ya rage farashin dala

. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan matakin zai iya kara karya darajar naira a kasuwar bayan fage

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya rage farashin dalar Amurkar da yake sayar wa mutane daga N375 zuwa N360.

A wani sako da bankin ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, ya ce zai fara sayar wa bankuna dala akan Naira 357 inda su kuma bankunan kasar za su fara sayar wa ga mutane kan Naira 360.

Babban bankin yana shiga kasuwar kudaden kasashen wajen ne domin rage gibin da ke tsakaninta da ta bayan fage.

A watan da ya wuce dai kasuwar bayan fagen na sayar da dala kan N520 bayan babban bankin Najeriya ya rage darajar naira zuwa 375 ga dala daya.

Faduwar darajar naira ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, abin da ya kara jefa jama'a cikin kunci.

Najeriya na fama da matsalar tattalin arzikin da ba ta taba samun kanta a ciki ba a shekara 20.

Farashin naira ya fara farfadowa ne tun bayan da bankin ya fara zuba kudi a kasuwar musayar kudade ta kasar.

An sayar da dala N315 a hukumance a ranar Litinin.

Asarar miliyan 130

Amma masu sana'ar canji kuma sun tafka asarar kudi naira miliyan 130 sanadiyyar faduwar darajar dala bayan babban bankin Najeriya (CBN) ya sayar da dala miliyan 25 kan N381 ga ko wace dala a makon jiya, in ji shugabansu na kasa, Aminu Gwadabe.

Shugaban 'yan canjin ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Rueters cewar mambobinsa za su iya kauracewa cinikin dalar da babban bankin Najeriyar ke son yi a wannan makon har sai ta kara nazari kan bambance-bambancen farashi a kasuwar kudin kasar.

A ranar Litinin ne babban bankin Najeriya zai kaddamar da dala miliyan 100 ta sayarwa, in ji masu sanar'ar canji.

Bayan bankin ta fara sayar da dala ne darajar dala ta fadi daga N520 a watan jiya zuwa N390 a kasuwar bayan fage.

Labarai masu alaka