Nigeria: Shin Saraki ya wawure naira biliyan 3.5?

. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bukola Saraki yana fuskantar shari'ah kan rashin bayyyana kadarori a kotun ɗa'ar ma'aikata ta Nijeriya

Shugaban Majalisar dattawan Nijeriya, Bukola Saraki ya musanta duk wani hannu a badaƙalar wawure naira biliyan 3.5 a cikin wasu kuɗaɗe na bashi da ƙasashen Paris Club suka yafe wa ƙasar.

Kafofin yaɗa labarai a Nijeriya dai sun bayar da rahotannin yadda wani rahoton hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar ta'annati EFCC ya shaida wa shugaba Muhammadu Buhari, cewar Sanata Saraki ya yi amfani da mataimakin shugaban ma'aikatansa da kuma wasu jami'ansa wajen halarta kuɗin haram.

Rahoton ya bayyana yadda Mista Saraki ya hada mataimakin shugaban ma'aikatansa da waɗanda suka tuttura kuɗaɗen zuwa asusun bankunan da ke da alaƙa da shi.

Rahoton na EFCC ya ce za a iya tuhumar shugaban majalisar da waɗanda suka taimaka masa da laifin halarta kuɗin haram.

Sai dai, mai taimaka wa Bukola Saraki a kan harkokin yaɗa labara, Yusuph Olaniyonu, ya musanta rahoton, yana mai cewar wani matakin ramuwar gayya ce daga muƙaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, wanda majalisar dattawan Nijeriya ta ƙi tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaba.

Rahotanni sun ce yayin da aka miƙa rahoton wannan badaƙala ga shugaba Buhari ranar 10 ga watan Maris, ita kuwa majalisar dattawan a ranar 15 ga watan ne ta ƙi tabbatar da Ibrahim Magu a mukaminsa.