An gano wata gawa a wata jaka a Italy

Jirgin ruwan yawon shakatawa Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption A tashar jiragen ruwan Rimini, wanda ke arewa masogabashin Roma aka gano akwatin da gawar ke ciki

'Yan sanda na bincike a kan ko gawar wata da aka gano a cikin wata jaka a tashar jiragen ruwa dake Italiya ta wata mata ce da ta bata, wadda ke zaune a Dublin.

Xing Lei Li, haifaffiyar China ta bata ne a cikin wani jirgin ruwa na yawon shakatawa a watan Fabrairu bayan ta hau jirgin a garin Genoa.

A watan da ya gabata ne aka kama maigidan Ms Li, Daniel Belling, a birnin Roma lokacin da yake kokarin hawa wani jirgin sama zuwa Dublin.

Lauyanshi ya dage a kan cewa gawar da aka gano a akwatin na da tsayi sosai balle a ce ta Ms Li ce.

Mista Belling ya dage a kan cewa ta fice daga jirgin ruwan na yawon shakatawa bayan sun yi wata 'yar hatsaniya, amma babu wata shaida da ke nuna cewa matarsa ta fita daga jirgin.

An ganor ta bata ne bayan ma'aikatan jirgin sun kirga mutanen da ke ciki bayan da ya isa inda zai sauke fasinjojinsa.

Ma'auratan suna hutu ne a lokacin da suka shiga jirgin ruwan mai suna MSC Magnifica da yaransu biyu, wadanda ke karkashin kulawar hukumar da ke kula yara ta Italiya.

A tashar jiragen ruwan Rimini, wanda ke arewa masogabashin Roma aka gano akwatin.

Nisan wurin dai zai kai mil 100 daga inda ake zato an kashe Ms Li kuma aka jefo gawarta daga cikin jirgin ruwan.

Manema labaran Italiya sun ce an gano gawar, wadda aka daddatsa ta ne a cikin wata bakar jaka da ma'aikatan tashar jiragen ruwan suka saka cikin wani akwati.

An yi amannar ta yi kwana goma da mutuwa.

Sai dai da yake musanta cewa gawar da aka gano ta yiwu ta Ms Li ce, lauyan Mista Bellings ya dage da cewa: "Tsayin gawar dake cikin akwatin sentimita 170 ne, amma matar Daniel Belling bata kai tsayin haka ba."

Babban mai shigar da kara na Rimini ya shaida wa manema labaran Italiya cewa suna gudanar da bincike tare da 'yan sandan Roma domin su gano ko gawar ta Ms Li ce.