'Yan kasuwar Sabon Garin Kano sun sake shiga rigima

Kasuwar Sabon Garin Kano Nijeriya
Image caption Iftila'in gobara ya jefa 'yan kasuwar Sabon Garin Kano cikin halin tsaka mai wuya

'Yan kasuwar Sabon Gari da ke Kano a arewacin Nijeriya sun gudanar da addu'o'in neman ɗauki sakamakon rashin samun tallafi bayan gobarar da ta laƙume dukiyarsu a bara.

Shekara guda kenan bayan wata mummunar gobara da ta ƙone kanti kimanin dubu huɗu a kasuwar da kuma haddasa asarar biliyoyin naira.

Wasu 'yan kasuwar sun ce rayuwarsu ta fada cikin wani mummunan hali tun bayan wannan gobara, yayin da masu bin bashi suka kai wasunsu gaban alkalai inda ake tafka shari'ah.

Daya daga cikin 'yan kasuwar Auwalu Isa Adamu ya ce masu binsa bashi sun je sun kwashe masa 'yan kayan da wani ya ba shi bashi don kada ya zauna zaman kashe wando a rumfarsa.

''Yanzu na abinci ma na yi min wahala, yau tsawon shekara guda kenan ba mu samu tallafi ba, gwamnati ta ce ta bayar da tallafin kudi amma ba a fadi lokacin da za a raba ba.''

Bayan aukuwar gobarar a bara, gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin tara gudunmawa a ƙarkashin attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote domin nema wa yan kasuwar da gobarar ta shafa tallafi. To sai dai wasu yan kwamitin da BBC ta tuntuba sun ce ko sau daya kwamitin bai taba zama taro ba, tun bayan ƙaddamar da shi a fadar gwamnati.

Gwamnatin jihar dai ta sanar da bai wa 'yan kasuwar tallafin naira miliyan 500, sai dai har yanzu kuɗin bai je ga hannun 'yan kasuwar ba.

Daya daga cikin jagororin kasuwar Sabon gari, Alhaji Alin Bagadaza ya bayyana cewa baya ga wannan kwamitin, suna kuma sauraron wasu bangarorin domin kai musu dauki game da mawuyacin halin da suka shafe shekara guda a ciki.

Labarai masu alaka