BH: Ɗumbin 'yan gudun hijira na neman ɗauki a Ibadan

'Yan gudun hijira a Nijeriya
Image caption Dubban mutane ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a yankin arewa maso gabashin Nijeriya

Ɗumbin 'yan gudun hijira daga yankin arewa maso gabashin Nijeriya da suka samu mafaka a Ibadan babban birnin jihar Oyo sun bukaci gwamnatin ƙasar ta kai musu dauki, don su koma gida.

Sun ce suna son koma wa garuruwansu na asali ne don samun saukin halin kuncin da galabaita sakamakon rashin tallafi da suke ciki.

'Yan gudun hijirar da ke samun mafaka a yankin kudu maso yammacin Nijeriya tsawon shekara uku, bayan ƙungiyar Boko haram ta rabo su da gidajensu a arewa maso gabashin kasar.

Suna kuma zaune ne sansanonin da gwamnati ba ta san da zamansu ba a jihar ta Oyo.

Joseph James wani dan gudun hijira da ya fito daga garin Gwoza kudancin jihar Borno ya shaida wa BBC cewa suna bukatar tallafin sana'o'i, da kuma buɗe musu hanyar koma wa garuruwansu.

''Yaranmu suna zube babu abinci, ba makaranta, muna cikin wani hali, gwamnatoci da kungiyoyi su taimaka mana," in ji shi.

Ita ma wata mata 'yar gudun hijira ta ce a cikin ɗumbin matsalolin da suke fuskanta akwai rashin kula da lafiyarsu, ta ce yayin da mace ta zo haihuwa (a cikinsu) ko dai a rasa jariri ko kuma ita kanta uwar.

'' Idan haihuwa ta zo wa mace sai dai a cikinmu mu taimaka mata, don ba mu da kudin zuwa asibiti.''

Mutane sama da miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Labarai masu alaka