Ba ni da ikon dawo da Ndume — Bukola Saraki

Sanata Bukola Saraki Hakkin mallakar hoto Other

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki, ya ce majalisa ce kadai ke da ikon dawo da Sanata Ali Ndume, wanda aka dakatar tsawon wata shida a makon da ya gabata.

Da yake magana bayan ya yi wata ganawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati, Mista Saraki ya ce daidai ya ke da sauran 'yan majalisar.

An dakatar da Sanata Ndume ne bayan da ya nemi a yi bincikekan rahoton da ke cewa Mista Saraki ya shigo da motoci ba bisa ka'ida ba, da kuma cewa Sanata Dino Melaye bai yi digiri ba.

Tuni dai kwamitin da'a na majalisar ya wanke mutanen biyu.

Tun bayan dakatarwar ne dai wasu 'yan siyasa ciki har da gwamnan jihar Borno, inda Ndume ya fito, suka yi kira ga Saraki da ya sauya matakin da majalisar ta dauka.

Sai dai ya ce abin da zai iya yi shi ne kawai ya shaida wa majalisa bukatar da gwamna Kashim Shettima ya gabatar masa domin ta dauki matakin da ya ga ya dace.

Ganawar ta Mista Saraki ya yi da Shugaba Buhari ta zo ne a daidai lokacin da takun-saka tsakanin bangaren zartarwa da majalisa ke kara ta'azzara.

Takun-sakar dai ta kai har majalisar dattawan kasar ta dakatar da tantance mutanen da shugaban ya nada kwamishinoni a hukumar zaben kasar.

Majalisar dattawan ta ce ta dauki matakin ne saboda shugaban kasar bai dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci ta (EFCC) Ibrahim Magu ba, duk da cewa majalisar ta ki ta tabbatar da shi.

Labarai masu alaka