Kun san 'yan Najeriyar da suka fara wasan tseren dusar ƙanƙara?

Wannan ne karo na farko da wasu 'yan Afirka suka gwada shiga gasar dusar kankara ta bobsleigh
Image caption Wannan ne karo na farko da wasu 'yan Afirka suka gwada shiga gasar dusar kankara ta bobsleigh

Shin tawagar Najeriya za ta bakuncin gasar tseren kankara wato bobsleigh, ta duniya da za a gudanar a Koriya ta kudu a 2018? Tuni dai an samu wasu tsoffin 'yan tsere uku wadanda 'yan Najeriya ne sun dauki aniyar shiga gasar.

Wannan ba wai zai zamo karo na farko da wata tawagar Najeriya za ta shiga gasar bobsleigh ba ne, zai zama karo na farko da wata tawaga a Afirka ta maza ko mata ta fara shiga gasar ne. Al'amarin da ya zama tamkar wani shirin fim.

Me ya sa suka zabi shiga gasar?

Wata tsohuwar 'yan tsere Seun Adigun ce jagorar tawagar. Matashiyar 'yar shekara 30 tana son nuna cewa ba wani abu da ba zai iya yiwuwa ba. Ita ce gwarzuwar 'yar wasan Najeriya da ta yi nasara a tseren mita 100 ta kuma wakilci kasar a gasar Olympic ta 2012.

Duk da cewa ta daina wasannin tsere, to ba ta shirya daina wasanni ba gaba daya tukunna. Ta shigar tawagar wasan bobsleigh ta Amurka, inda bayan ta yi bincike sosai, sai ta sha mamaki lokacin da ta gano cewa Afirka ba ta taba samun wakilci a gasar Olympic ta lokacin hunturu ba.

"Muna da kokari, kuma muna da duk wani abu da muke bukata wajen yin hakan, muna da shaukin wasan, muna da kwarin gwiwa, muna da masu koyar da wasan, mun iya tseren, to me ya sa ba za mu yi ba?" in ji ta.

Bayan dogon nazari sai kawai ta yanke shawarar gwada sa'arta a wasan bosbleigh a watan Satumbar 2016. A yanzu haka tana fatan ta koyawa mutanen da ke da sha'awar wasanni a nahiyar Afirka irin abin da ta koya.

Ina son fada wa 'yan Najeriya cewa suna da wani abu da za su yi alfahari da shi, kuma abinda za mu zo muku da shi, wani abune da zai shiga zukatanmu, wadannan mata ukun yanzu an kusa a sanya sunansu a kungiyar tsere ta mata ta Afirka. Muna son gaya wa 'yan Najeriya cewa muna alfarin daukar tutar kasar, kuma babu wani abu mai muhimmanci a garemu yanzu illa mu ga kasarmu ta samu kyakkyawan wakilci a gasar.

Gwaji ba a kan dusar kankara ba

Seund Adigun na son daukar tsohuwar 'yar tseren Najeriya Ngozi Onwumere, wacce ta ci kyauta har sau biyu a gasar Afirka da kuma Akuoma Omeoga wacce ta wakilci Jami'ar Minnnesota. Ngozi ta amince da shiga cikin tawagar kafin ma ta fahimci abin da ta kunsa.

"Ni sabuwar kamu ce a wasan. Ban san komai ba game da tseren kankara sai dai na riga na amince da kwantiragin. Kuma ban san komai ba game da tsere, ballantana in yi muku karya, ban san komai ba, ban ma san abin da wasan ya kunsa ba, da abin da ake bukata, yanzu ne na sani, amma ta dauke ni, na yi sa'a na samu abinda take so".

Atisayen da Seun Adigun take yi wa mata biyun, ya sa sun samu kansu tamkar a wani sabon aji na koyon sabon darasi. Tawagar na can birnin Houston ne a jihar Texas ta Amurka, wurin da ake ganin yafi ko ina cancanta da atisayen gasar.

Amma dole 'yan tseren su sake jajircewa wajen yin atisaye don kai wa gaci. An sanyawa kungiyar suna "Maeflower", wato sunan wata kanwar Seun da ta rasu. A ganin daya daga cikin 'yan tseren Akuoma, yana da matukar muhimmanci a tunatar da sauran kasashe wadanda ke ganain su ba su da karfin gwiwar fafatawa a gasar.

"Ba mu da abubuwan da za mu fara wasan da su, to amma mun kirkire su, ba mu da yanayin da zai bamu damar yin atisaye to amma za mu yi atisayen kamar yadda wasan ke bukata, don haka za mu zama abin misali kuma za su ga ashe za su iya wanna aiki, ko da kuwa suna ganin kamar ba za su iya ba," a cewar Akuoma.

Atisaye a kankara

Lokaci-lokaci tawagar Najeriyar kan yi atisayen wasan bobsleigh a cikin tsananin hunturu. A baya-bayan nan tawagar ta ziyarci Calgary a lardin Alberta a yammacin Canada a atisayen Seun na karshe a kakar wasannin. Masu tseren za su yi gudun mita 1600 a kan kankara da wani dan zafi da bai haura digiri 18 na matakin selshiyas ba, wanda kuma hakan kalubale ne ga Ngozi.

"Kasancewata daga Texas, hakan ya zama min wani al'amari na zage dantse sosai. Ina tsammanin sakamako mafi muni idan aka zo batu na yanayi, amma dai za mu yi kokari, idan ka fara gudun za ka ji jikinka ya fara daukar zafi, kuma hakika sinadarin adrenaline zai saka samun karin zafi."

A bangaren Seun, wanna dama ce a gareta ta kara inganata kwarewarta a matsayin 'yar tseren kankara. Masu tsren kankara dai na amfani da wani kaya "uniform" wanda ke dauke da hular kwano domin kariya wajen yin kwana, kuma Seun tana shan wahala wajen amfani da su da farko.

"Ina fama da ciwo kuma jikina ya kan dauki ciwo gaba daya, amma kuma dole haka za a cije a ci gaba, kamar wani ne ya sanya ka kan wani babban tsauni kuma ya sako ka kasa."

A karshe masu tseren kankara basa bata lokaci mai yawa a kan kankarar. A lokutan atisaye su kan maida hankali ne wajen tara karfin da za su yi amfani da na'urorin wanda ke da nauyin kilogiram 170.

"Akwai abubuwa da dama game da wasan, dole ka zama mai karfi kuma mai sauri domin fara wasan, dole ka zama mai kaifin kwakwalwa, kuma mai tunani, idan wani abu ya faru kuma wannan abun ya faru a kanka dole ka rike shi, dole ka zama mai ilimi sosai domin tukin yana kama da hadarin mota," in ji Sarah Monk wata tsohuwar mai koyar da tseren a Calgary kuma tsohuwar 'yar tseren da ta wakilci Canada.

Wasa mai tsada

Image caption 'Yan matan uku da suka shiga gasar Bobsleigh

Kafin Najeriya ta samu shiga wannan gasar, tana bukatar samun isasshen kudi don cima burinsu. Sun kaddamar da wani asusun neman tallafi daga mutane a watan Nuwambar 2016 da nufin samun dala 150,000. Zuwa yanzu dai da kyar suka tara dala 16,000. Kayayyakin da ake bukata suna da matukar tsada, wanda hakan ke nufin kasashe kadan ne za su taka rawa a wasannin.

Amma tawagar Najeriya na fatan shigarsu cikin gasar zai sa a samu wayewar kai sosai kan wasan bobsleigh.

Baya ga haka kuma dole 'yan wasan su raba lokacinsu wajen yin atisaye da sauran al'amuransu na yau da kullum.

Sai dai Seun da Ngozi da Akuoma ba za su iya zama 'yan wasan bobsleigh na din-din-din ba. Seun daliba ce ta wani bangare na lafiya, don haka bata da isasshen lokacin da za ta ware don yin wasan bobsleigh.

Sai dai duk da rashin isasshen lokaci da suke da shi, su kan ware wani lokaci don yin atisayen da kuma yin nishadi, inda su kan sanya wakokin Najeriya masu dadi su cahse rawa a dakinsu.

Labarai masu alaka