An far wa 'yan Nigeria hudu a Indiya

Afrin students in India Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daliban Afirka suna yawan korafin cewar an musu wariyar launin fata a Indiya

An ji wa 'yan Najeriya hudu ciwo a Indiya bayan an kai musu hari a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin kasar, a wani hari na baya-bayan nan da aka kai kan 'yan Afirka a kasar.

Ministan harkokin wajen kasar, Sushma Shawaraj, ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter cewar gwamnar jihar ta Uttar Pradesh ta tabbatar da cewar za ta yi binciken ba-sani-ba-sabo kan lamarin da ta kira na takaici.

Jaridun Indiya sun bayar da rahoton cewar an kama mutum biyar da ake zarginsu da hannu a harin a birnin Greater Noida.

Da farko dai fiye da mtum 100 ne suka yi zanga-zanga a wata tashar motocin bas a birnin, suna masu neman a kori duk 'yan Afirkan da ke zama a gidajen haya a unguwannin da ke Greater Noida, kamar yadda jaridar Indiyan Express ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne bayan wani dalibi ya mutu bisa dalilin da ake tunanin na shan kwaya ne.

An daure daliban Najeriya biyar kan lamarin, amman an sake su domin rashin hujja, in ji jaridar.

A shekara da ta wuce dai wasu ofisoshin jakadancin kasashen Afirka sun yi korafi ga gwamnatin Indiya kan wasu jerin hare-haren da ake kaddamarwa kan dalibai daga Tanzaniya da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

Labarai masu alaka