Nigeria: Majalisa ta juya wa Buhari baya kan nadin Magu

. Hakkin mallakar hoto FEMI ADESINA/ FACEBOOK
Image caption Majlisar dattawan Najeriya tana takun-saka da wasu hukumomin bangaren zartarwar kasar

Majalisar Dattawan Najeriya ta ki tabbatar da sunayen wadanda shugaban kasar, Muhammadu Buhari, ya nada a matsayin kwamishinonin hukumar zaben kasar INEC.

Majalisar ta yi hakan ne a wani mataki na ramako ga bangaren zartarwar kasar kan ci gaban mukadashin shugaban hukumar yaki da cin hanci ta EFCC da zama a kan kujerarsa bayan 'yan majalisar sun ki tabbatar da shi.

Zaman majalisar na ranar Talata, wanda shugabanta Bukola Saraki ya jagoranta, ya dakatar da nazari kan sunayen kwamishinonin INEC 27 din da Buhari ya tura majalisar ne har sai bayan mako biyu.

Daga farko dai 'yan majalisar sun nemi hana majalisar magana kan tantance sunayen kwamishinonin ne gaba daya, amman daga baya Sanata Saraki da mataimakinsa Ike Ekwerenmadu, sun nemi 'yan majalisar su yi hakuri a dakatar da tantancewar na wucin gadi.

Bayan haka ne Sanatan da ya gabatar da kudirin dakatar da tantancewar, Sanata Peter Nwaboshi da ke wakiltar Delta ta Arewa, ya gyara kudirin nasa, kuma majalisar ta amince da hakan.

Wasu daga cikin 'yan majalisar sun yi ikirarin cewar mukadashin shugaban hukumar EFCC yana musu bita-da-kulli bayan sun ki tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar.

A ranar Ltinin ne dai kafafan yada labaran kasar suka byar da rahoton cewar Ibrahim Magu ya mika wa shugaban kasar, Muhammadu Buhari, wani rahoton da ke cewa shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki, ya wawushe naira biliyan 3.5 a cikin kudin lamunin Paris Club din da aka mayarwa Najeriya.

Amman Saraki ya musanta hakan yana mai cewar ramakon gayyan ne mukaddashin shugaban EFCC ke yi don kin tabbatar da shi a kan mukaminsa.

Rahotanni dai sun ce an mika wa Shugaba Buhari rahoton na EFCC ne ranar 10 ga watan Maris inda Majalisar Dattawan kasar ta ki tabbatar da Ibrahim Magu a mukaminsa ranar 15 ga watan na Maris.