Ya ya aiki da Sashen Hausa na BBC yake?

Albarkacin cikar sashen Hausa na BBC shekara 60, wasu daga cikin ma'aikatanmu sun fadi irin tasirin da aiki da BBC yake yi a rayuwarsu.

Ga dai wasu mutum 10 daga cikin ma'aikatan da abin da suke fada dangane da hakan.

Image caption Sulaiman Ibrahim Katsina ya dade yana aiki da BBC Hausa a yanzu haka dai babu wanda ya fi shi dadewa cikin ma'aikatan sashen

Ga abin da yake cewa kan aiki da BBC: "Ina ganin aikin BBC a matsayin wata babbar dama ta taimakawa wajen wayar da kan al'ummata da kuma inganta harshen Hausa. Wayar da kai ya hada da sanar da jama'a abin da gida da duniya suke ciki da kuma abubuwan da za su amfane su ko cuce su.

Inganta aiki da harshen Hausa na da matukar muhimmanci, musamman da yake ba dukkan matasa ne suke koyon harshen sosai ba a wannan zamani.

Image caption Aliyu Tanko ya fara aiki da sashen Hausa na BBC a shekarar 2008 a Abuja, kuma tun daga lokacin ya yi ayyuka da dama a fannoni daban-daban

Aliyu ya ce, "Ina matukar alfahari da farin cikin kasancewa ma'aikacin wannan kafa saboda wuri ne da na kara gogewa da aikin jarida sannan kuma na fadada ilimina a ayyukan da suka shafi harkokin intanet da wayar salula da kuma shafukan zumunta na zamani.

"A cikin 'yan shekarun nan, BBC ta tura ni kasashe daban-daban domin aiko da rahotannin abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum, sannan ba zan manta da lokacin da ne je kasar Afrika ta Kudu ba a shekarar 2010, inda na halarci gasar cin kofin duniya ta farko da aka yi a Afrika.

"Na koma ofishinmu na London sama da shekaru biyar da suka wuce, inda bayan wasu shekaru a yanzu haka na ke aiki a fannin turancin Ingishi na Newsday domin karin samun gogewa."

Image caption Habiba Adamu ta fara aiki da sashen Hausa na BBC a shekarar 2016

Ta ce, "Aiki da sashen Hausa na BBC abu ne da ko wane dan jarida zai yi fatan samun kansa a ciki, saboda BBC kafar yada labarai ce da ta yi zarra kuma ta ke sahun gaba a duniya. A shekarun da na shafe a BBC, na koyi darasi da dama na rayuwa, kuma mafi muhimmancin su shi ne fadin gaskiya komai dacinta."

Image caption AbdusSalam Ibrahim Ahmad shi ne wakilin BBC a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya

"Aiki da BBC wata dama ce ta gudanar da aikin jarida bisa ka'ida da adalci, da fadar gaskiya, da bayyana hoton abin da ya auku ba tare da son zuciya ko bangaranci ko kiyayya ko kuma fadanci ba". A cewar AbdusSalam Ibrahim Ahmed.

Image caption Tchima Illa Issoufou ta fara aiki da sashen Hausa na BBC a watan Satumbar shekarar 2009, ita ce wakiliyar BBC a Damagaram ta Nijar

Ta ce, "Aiki da BBC a wajena wani abu ne da na sa kaina da kuma na ke jin dadinsa, saboda an ce bawan yarda ya fi bawan saye, hakan ya sa ba na jin wani tsoro, ko damuwa cikin wannan aiki da zarar dai kan gaskiya nake. Amfanin wannan aiki a gare ni shi ne cewa duk inda na je da an ce Tchima ce ta BBC, mutane za su yi ta nuna jin dadinsu na gani na, musaman mutanenmu na karkara suna gode mani suna mani addu'a.

"Sai dai ni ba ni da farin jini a wajen hukumomi. Ina karuwa sosai da yadda nake kara samun gogewa a fannoni da dama na aikin jarida ta hanyar taya ni gyaran kura-kurai da abokan aikina musamman na Abuja ko London ke yi."

Image caption Ibrahim Isah ya fara aiki da BBC a shekarar 2008

Ya ce, "Aiki da BBC na da dadi saboda ana bunkasa ma'aikaci, tare da sakar masa mara wajen yin labari a kan kowa komai girman mutum ko hukuma, matukar baka saba wa ka`idar aikin jarida ba. Ina samun gamsuwa da yadda BBC ke bayar da fifiko ga talaka ko wanda aka zalunta ko kuma al`umar da take da rauni da nufin tabbatar da adalci a tsakanin jama`a."

Image caption Aichatou Moussa ta fara aiki da BBC a shekarar 1998

Ta ce, "Idan aka kwatanta da lokacin da na zo aikin ya sauya sosai. An samu ci gaba ta fannoni daban-daban kamar rediyo da intanet da shafukan sada zumunta da kuma talbijin. An ba mu horo sosai a wadannan fannoni, don haka zan iya cewa kafar yada labarai ta BBC daya ce tamkar da goma. Idan dai batun ci gaba ake da neman kwarewa a fannin jarida, to lallai BBC tana sahun gaba."

Image caption Bilkisu Babangida wadda a da wakiliyar BBC ce a Borno amma a yanzu tana ofishin Abuja

"Na fara aiki a wasu kafafen yada labarai kamar su gidan rediyon Kano, da Radio Nigeria da kuma Muryar Amurka, amma gidan rediyon BBC ba shi da na biyu a wajena domin a nan ne na kara samun kwarewa a fannin aikin jarida a fannoni da dama. Zan iya kiran gidan rediyon BBC tamkar wata makarantar da ke sa gogewa a fannin aikin jarida. Ina alfahari da kasancewa ta ma'aikaciyar BBC a duk inda nake." Kalaman Bilkisu Babangida kenan.

Image caption Yusuf Tijjani ya fara aiki da BBC a shekarar 2008

Yusuf Tijjani ya ce, "Ina matukar alfahari da kasancewa daya daga cikin ma'aikatan sashen Hausa na BBC, musamman irin horo da gogewa da na samu a harkar watsa labarai. Kuma hakika aiki da nake yi a sashen Hausa na BBC ya ba ni damar haduwa da jama'a da dama a ciki da wajen Nigeria wanda kuma zai ci gaba da tasiri a rayuwata." 

Image caption Nurah Muhammad Ringim, wakilin BBC Hausa a Kaduna

"Aiki da BBC Hausa ya matukar kara min kwarewa a fannin aikin jarida. Na fara aiki da BBC ne bayan na shafe wasu shekaru ina aikin jarida da wasu kafafen yada labaran da kuma wasu bangarorin kamar koyarwa da aikin banki. Amma a gaskiya na fi samun karin kwarewa da iya mu'amala sosai a shekarun da na yi ina aiki da BBC fiye da sauran ayyukan," in ji Nurah Muhammad Ringim.

Labarai masu alaka