Kun san yadda ɓera ya fara rayuwa da mutane?

Mage da bera Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana samun beraye a gidaje mutane a sassa-sassan duniya

Binciken wasu kasusuwan ɓeraye da aka gano ya nuna cewa ɓera ya fara rayuwa a cikin mutane tsawon shekara 15,000 da ta gabata.

Masana kimiyya sun yi amannar cewa berayen jeji sun shiga cikin lardin gabashin Bahar-rum suka yi satar tsabar da ake samu a daji da kuma irin da mutanen da suka tara kuma suke ajiyarsu.

Berayen wancan lokacin ne muka sani a matsayin berayen da ke gidajenmu wadanda suka baje kuma suke cinye abincin gidajenmu.

"A yanzu, berayen gida sun samu wayewar kai kuma suna sassan duniya daban-daban kamar dai mutane, a cewar Dakta Thomas Cucchi da ke gidan adana kayan tarihi na d'Histoire naturelle da ke birnin Paris.

Ya yi binciken ne kan hakoran wasu beraye da aka gano a kudancin Levant, da ke bahar-rum.

Dakta Thomas ya ce beraye sun fara rayuwa tare da mutane ne tun lokacin da mutane suka fara gina gidaje a shekaru 15,000 da suka wuce.

A wancan lokacin mutane na zama ne a gidajen kara da laka. Su kuma berayen na neman abincin da ya danganci tsaba sannan kuma suna farautar barewa da dai sauransu.

Berayen sun ji dadin rayuwarsu a wannan yanayin saboda suna samun isasshen abinci da kuma dabbobin da suke farautarsu. Sai daga baya ne maguna da karnuka suka isa wurin.

Abin sha'awar shi ne, akwai abubuwan da ke nuna alamun ana ajiye karnuka a gidaje.

Dakta Jeremy Searle na jami'ar Cornell da ke Amurka, wanda ke da alaka da binciken da aka gundanar, ya ce binciken ya yi karin haske a kan dangatakar harkar noma tsakanin berayen gida da mutane.

Duk da cewa dabbar jeji ne, beran gida na zama ne tare da mutane.

Suna nan a gidajen mutane da dama a matsayin dabbar da aka saba da ita, ake kuma amfani da shi wajen gwaje-gwaje a dakin gwaji a asibiti.

Yana kuma da muhimmanci wajen gudanar da wasu binciken lafiya da ake yi.

Labarai masu alaka