DR Congo: An gano gawawwakin jami'an MDD

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An shafe watanni ana dauki ba dadi a yankin Kasai na Jamhuriyar Congo bayan kisan wani basarake

An gano gawawwakin wasu kwararru na Majalisar Dinkin Duniya biyu da aka sace makonni biyu da suka gabata a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Kakakin gwamnatin kasar ta Congo Lambert Mende ya tabbatar wa BBC aukuwar lamarin.

Ya ce an gano gawawwakin na Michael Sharp wanda Ba'amurke ne, da kuma Zaida Catalan 'yar kasar Sweden a tsakiyar yankin Kasai.

A makonni biyu da suka gabata ne aka sace jami'an bayan da suka je yankin Kasai don gudanar da bincike kan rahotannin cin zarafin bil'adama, bayan da 'yan tawaye suka dauki makamai.

A karshen makon da ya gabata ma, an gano gawawwakin wasu jami'an 'yan sanda 40 a yankin bayan an datse kawunansu

Daga bisani ya shaida wa manema labarai cewa kwamishinan 'yan sanda ya dawo daga yankin na Kasai, inda ya tabbatar da ƙasashen da mutanen suka fito.

An sace Mr Sharp da Ms Catalan ne tare da wasu mutane hudu 'yan kasar Congo masu aiki da Majalisar Dinkin Duniya inda aka kai su zuwa cikin wani daji da ke kusa da kauyen Ngombe a yankin Kasai.

Gwamnatin jamhuriyar Congo tana fafatawa da kungiyar 'yan tawaye da ke aikata ta'asa a yankin, wadda aka yi amanna mayakanta ne suka sace tare da hallaka kwararrun.

An shafe watanni ana dauki ba dadi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye a yankin, bayan kisan wani basarake Kamuina Nsapu, wanda ke jagorantar boren nuna kin jinin shugaba Joseph Kabila.

Labarai masu alaka