Masu sanƙarau sun ce magani sai wane da wane

Sankarau a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A yankin Zurmi cikin jihar Zamfara, yara kimanin ashirin aka ba da rahoton cewa sun mutu sakamakon sanƙarau

Masu fama da cutar sanƙarau a wasu yankuna kamar Zurmi a jihar Zamfara ta Nijeriya ba sa iya samun magani kyauta a asibitoci duk da annobar da ake fama da ita.

Zamfara ita ce jihar da ta fi fama da mutanen da suka kamuwa da cutar sanƙarau baya ga waɗanda suka mutu sakamakon wannan cuta.

Daraktan taƙaita yaɗuwar cutuka a ma'aikatar lafiya ta tarayyar Nijeriya, Dr. Nasir Sani Gwarzo ya ce sanƙarau ta yi sanadin mutuwar mutum 86 a jihar ya zuwa ranar Litinin, baya ga ƙarin wasu 590 da ke jinya sakamakon kamuwa da cutar.

Jami'in lafiyar ya ce kusan babu ƙaramar hukumar jihar da ba ta fuskantar wannan cuta yanzu a Zamfara.

Wani mazaunin yankin ya faɗa wa BBC cewa a ƙiyasi kimanin yaro ashirin ne suka mutu a yankin Zurmi sakamakon cutar sanƙarau.

Ya ce "Fisabilillahi! A tsakani da Allah, wannan ciwo yana halakar da mutane. Akwai yara biyu da suka rasu ba a fi kwana biyu ba yanzu.

Kuma idan ka je asibitai, duk mun kai 'ya'yanmu gwargwadon hali, mun dawo da wasu, su ma maƙwabta suna kai nasu."

Malamin makarantar wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce ya zuwa ranar Talata, sai sun sayi magani a asibiti, idan sun kai 'ya'yansu.

A cewarsa, gwamnati ba ta kai magunguna da alluran riga-kafi zuwa yankin ba tukunna, don kuwa shi da kansa ya kai wani ɗan ƙaninsa asibiti kuma sayen maganin suka yi.

Shi dai daraktan taƙaita yaɗuwar cutukan, ya ce gwamnatin ƙasar na yi bakin iyakar ƙoƙarinta don ganin ta shawo kan wannan annoba.

Dr. Nasiru Sani Gwarzo ya ce ya zuwa ranar Talata sama da mutum 150 ne suka tabbatar sun mutu, yayin da wasu kimanin 1,100 suka kamu da ita a faɗin ƙasar.

Tun da farko, jami'in ya ce jiha biyar ce aka tabbatar da ɓullar annobar ta sanƙarau ciki har da Sakkwato da Neja da Kano da kuma babban birnin ƙasar Abuja.

Labarai masu alaka