Maciji ya hadiye wani mutum a Indonesia

Mutum a cikin Mesa. Man inside the python Hakkin mallakar hoto West Sulawesi Police
Image caption An farka cikin mesar aka ga mutumin a ciki.

'Yan sandan wani gari a Indonesiya sun ce an gano wani mutum da ya bata a cikin wani katon maciji.

Mutumin mai suna Akbar ya bata ne a ranar Lahadi a tsibirin Sulawesi, bayan da ya bar gonarsa ta kwakwar manja don zuwa gida.

Wani dan sanda ya shaida wa wakilin BBC na Indonisiya cewa, ana tsaka da neman mutumin mai shekara 25, sai aka samu wata katuwar Mesa da ake zargin ita ce ta hadiye shi.

Rahotanni sun ce tsawon Mesar zai kai mita bakwai, an kuma farka cikinta inda aka samu gawar mutumin.

Mesa na daya daga cikin dabbobi masu jan jiki da suka fi tsawo a duniya, kuma su kan makure duk halittar da suka kama kafin su hadiye shi gaba daya.

Mesa ba ta cika kashe ko cin mutane ba, ko da yake a kan samu rahotonni a wasu lokuta cewa suna yara ko dabbobi.

Hakkin mallakar hoto West Sulawesi Police
Image caption Wata gabar jikin mutumin da aka samu da ba ta narke ba a cikin Mesar

Mai magana da yawun 'yan sandan yammacin lardin Sulawesi, Mashura, ya shaida wa wakilin BBC na Indonisiya cewa mutanen da ke garin sun kai rahoton batan Akbar cikin sa'a 24 da batansa.

Daga nan ne 'yan sandan suka gudanar da bincike inda aka gano Mesar a kusa da gonar kwakwar manjat tasa.

Mashura ya ce, "Ba su samu mutumin da ake nema ba mai suna Akbar, sai dai mutanen garin sun ga wata Mesa da ta kasa tafiya a wurin da ake ban ruwa, sai suka fara zargin wata kila Mesar ce ta hadiye Akbar. Da suka farka cikin Mesar ne suka gan shi a ciki."

Nia Kurniawan daga Jami'ar Brawijaya, ya shaida wa wakilin BBC na Indonisiya cewa, Mesar da ke da wannan girman za ta iya farautar manyan dabbobi ko karnukan daji.

Duk da yake Mesa ba ta cika son zama a wjen da jama'a suke ba, za ta iya yiwuwa suna ganin gonar kwakwar manja a matsayin wurin da ya dace da yin farauta, kamar yadda suke ribatar dabbobin da suka hada da birrai ko karnuka.

Labarai masu alaka

Karin bayani