Rahoton Ibrahim Dosara kan satar shanu a Zamfara
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Rahoton Ibrahim Dosara kan satar shanu a Zamfara

Satar shanu, a sassa daban-daban na Najeriya, wata matsala ce da ta janyo asarar rayuka da dukiya, barayin shanu dai sun rika amfani da miyagun makamai da ta'addaci wajen aikata ta'asar.

Zamfara na cikin jihohin da wannan matsala ta yi wa mummunan ta'adi ta fuskoki daban-daban, kama daga lalata muhallai da dukiya har ma da rayuwar dumbin mutane.

Ga rahoto na musamman da tsohon abokin aikinmu Ibrahim Dosara ya aiko mana daga jihar Zamfara, a matsayin tasa gudummawar kan bikin cikar sashen Hausa na BBC shekara 60.